Gabanin wannan dandali ne aka shirya wani zaman taro da ya hada kwararru na kwamitin kasa da kasa na kungiyar tattalin arziki da kudi ta tsakiyar Afrika CEMAC da aka bude ranar Laraba a babban birnin Congo da zai baiwa mahalarta taron damar maida hankali kan kasafin kudin tafiyar da ayyukan kungiyar a shekarar 2012.
Haka kuma taron wata babbar dama ce dake muhimmanci ta aiwatar da jadawalin aiki na tsarin tattalin arzikin shiyyar wato PER.
A yayin da yake bude ayyukan taron, ministan gyare gyaren kasar Congo Jose Rodrigue Ngouonimba ya gayyaci kwararrun da su gudanar da ayyukansu cikin tsanaki da kwarewa ga abubuwan da za'a tattaunawa kansu bisa jadawalin taron.
"Kasafin kudin an aiwatar da shi cikin yanayi na mawuyacin hali" in ji mista Ngouonimba. Amma duk da haka, ministan ya nuna fatan ganin an cimma wani sakamako mai kyau ga makomar shiyyar tare da yin amfani da tsare tsaren da suka wajaba, da cimma kasafin kudi mai karfi da daidaici ta yadda za'a gina wani harsashi mai nagarta cikin hadin kai ta yadda wannan yanki zai kasancewa wata babbar mahadar bunkasuwa.
A tsawon ayyukan taron, kwararrun za su maida hankali bisa batutuwan da suka fi janyo hankalinsu musamman kan batutuwan da ke da nasaba da harkokin kudi na jama'a cikin CEMAC, hadewar kungiyoyin tattalin arziki da kuma batun rikicin kudi na duniya.
Kungiyar CEMAC tana kunshe da kasashe shida wadanda suka hada da Kamaru, Congo, Chadi, Gabon, Guinee-Equatorial da kasar Afrika ta Tsakiya kuma cibiyar kungiyar tana birnin Bangui na Afrika ta Tsakiya.(Maman Ada)




