A cewar wani rohoto na tawagar dindindin ta kasar Congo dake MDD da aka baiwa manema labarai, manyan mutanen biyu sun nuna jin dadinsu a fili a yayin wata ganawa ta bangarorin biyu a gabanin zaman taron MDD karo na 66, wanda a yayin ganawar suka tattauna halin kasar Congo, a wannan yanki, a nahiyar Afrika da ma duniya baki daya.
A game da jamhuriyar kasar Congo, mutanen biyu sun nuna yabo kan yadda aka gudanar a kasa da kasa na Afrika game da harkokin internet, da dunkulewar kasa mai yanci, niyyar mai dorewa ta kasar Congo wajen kare hakkin bil'adam a duk fadin kasar da ma duniya, musammun ma a matsayinta ta mambar kwamitin kare hakkin dan adam a MDD, da wanzar da tsarin demokaradiya, rohoton ya kara da cewa.
Game da wannan yanki da ma duniya, mista Ikouele da Ban Ki-moon sun tabo batutuwan da suka shafi tsaron Afrika ta tsakiya, da duniya tare da tabo batun kawo sauye sauye a MDD. Haka sun yi shawarwari kan halin da kasar Libya ke ciki a gabanin wani babban taro da majalisar zata gudanar a ranar Talata a birnin New York. (Maman Ada)




