Cikin kokarin kungiyar ya hada da samun damar isa wajen da fashewar ya abku don su tabbatar ba ya cikin wani hadarin sannan kuma ta hada iyalai da suka bace ma juna musamman taimaka ma yaran da suka bace ma iyayensu a dalilin hadarin, in ji sanarwar da ta fito daga wajen kungiyar.
A karkashin yarjejiniyar da ma'aikatar tsaro ta jamhuriyar Kongo din, kwararrun masanan game da warware matsalolin da ya shafi albarusai sun rigaya sun isa Brazzaville ranar laraba da ta gabata kuma tuni har sun fara aiki tare da wadansu kungiyoyi don share wannan sansani.
Manufar masanan shi ne su tabbatar yankin baya cikin hadari saboda jama'a su samu daman komawa gidajensu cikin lokaci kuma ma'aikatan ba da agaji su samu damar shiga wannan yankin. (Fatimah)




