Kasar Togo ta bayar da agajin abinci da magunguna ga wadanda fashewar makamai ta rutsa da su a kasar Congo Brazzaville
A ranar 12 ga wannan wata, wani jami'in gwamnatin kasar Togo ya furta cewa, a wannan rana gwamnatin kasar ta fara jigilar shinkafa da magungunan da suka kai ton 50 zuwa ga wadanda hadarin fashewar –dakin ajiye makamai ya rutsa da su a Brazzaville. Kayayyakin agajin sun kunshi shinkafa ton 45 da magunguna.Wannan jami'i da bai fadi sunansa ba ya ce, gwamnatin kasar Togo tana kuma shirin tura wata tawagar likitoti zuwa birnin Brazzaville don taimakawa asibitocin kasar wajen ceton rayukan wadanda suka samu rauni a fashewar bama baman.
A ranar 4 ga wannan wata ne dai a Brazzaville, babban birnin kasar Congo, aka samu fashewar wani dakin ajiyar makamai, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane fiye da 200, a yayin da wasu sama da 1500 suka ji rauni. (Hauwa)