in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jaddada wajibcin kyautata muhimman kayayyakin kiwon lafiya a duniya
2013-05-14 10:39:04 cri

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO da asusun taimakon kananan yara na MDD UNICEF sun ba da wani rahoto a ran 12 ga wata a birnin Geneva na kasar Switzerland cewa, ya zuwa shekarar 2015, yawan mutane da ba sa samun muhimman kayayyakin kiwon lafiya zai kai biliyan 2.4, wanda ya kai daya cikin uku na adadin mutane a duniya.

Wannan rahoto mai jigon "Halin da ake ciki a duniya dangane da kayayyakin kiwon lafiya da ruwan sha na shekarar 2013" ya bayyana cewa, a cikin watan Maris na shekarar bara, WHO da UNICEF sun sanar da cewa, yanzu an cimma burin dake cikin shirin muradun karni na MDD ta fuskar rage rabin yawan mutane wadanda ba su samu ruwan sha mai tsabta ba kafin shekarar 2010, amma kasa da kasa na kasa samun ci gaba wajen kyautata muhimman kayayyakin kiwon lafiya. Ya zuwa yanzu, mutane kimanin kashi 64 bisa dari ne kawai suke samun wadannan kayayyaki masu inganci, lamarin da ya sa ba za a iya cimma wasu buri dake cikin shirin muradun karni na MDD cikin lokaci ba da ya shafi wannan fanni. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China