A cikin takardar, an ce, Sin ta dora muhimmanci sosai game da kiyayewa da kulawa da lafiyar jama'a, a cikin shekaru da dama da suka gabata, Sin tana kuma dagewa kan mayar da batun raya harkokin kiwon lafiya a kauyuka, da yin rigakafi gaban kome, da ma yin amfani da likitancin gida da waje, tare, da dogara da kimiya da ilmi wajen raya harkokin kiwon lafiya. Ta hakan ne, za a iya kokartawa wajen raya sha'anin kiwon lafiya da ke da halayyen musamman na kasar Sin. Bayan daukar wadannan matakai, yanzu, ana kara kafa tsarin harkokin kiwon lafiya a kasar, kuma aka sanya kwazo sosai a fagen yaki da cututtuka, baya ga kuma tsarin ba da inshora game da harkokin kiwon lafiya dake kara fadada a kasar.
Haka kuma, takardar ta bayyana cewa, harkokin kiwon lafiya na Sinawa yana sahun gaba a cikin kasashe masu tasowa, kuma an kiyasta cewa, matsakaicin tsawon rayuwar al'ummar kasar Sin ya kan kai shekaru 74.8.
Bugu da kari kuma, a cikin takardar, an ce, bayan da aka yi allurar rigakafi, yanzu, yawan mutanen da suka kamu da cututtuka ya kai matsayi mafi kankanta cikin tarihin kasar. Ya zuwa shekarar 2011, yawan mutanen da suka kamu da cutar kanjamau bai wuce dubu 780, adadin da ya yi kasa da hasashen da aka tsara, wato rage yawan al'ummar da suke kamuwa da cutar da yawansu ya yi kasa da miliyan 1.5.
Hakazalika kuma, takardar ta ce, gwamnatin Sin ta bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2020, za a kafa tsarin kiwon lafiya da ya shafi mutane a birane da garurruwa, don kowa ya more tsarin kiwon lafiya a kasar. Don haka, Sin za ta ci gaba da inganta aikin gyare-gyare, da kokarin raya harkokin kiwon lafiya, don tabbatar da lafiyar jama'ar kasar, kana za ta ci gaba da shiga aikin kiwon lafiya na duniya, don yin hadin gwiwa da ragowar kasashen duniya, wajen kara ba da babbar gudummawa game da harkokin kiwon lafiyar bil'adama.(Bako)