Hakan ya kawo adadin wadanda ke da laluran tabin hakali da gwamnati ta ma rajista a asibitoci daban daban a cikin shirinta na inshorar lafiya da take a cikin watanni fiye da 4 zuwa 10,000.
Shugaban shirin inshorar lafiya na kasar Sylvester Mensah ya ce, hakan na cikin tsarin gwamnati na walwala da kuma demokuradiyya don tabbatar da masu rauni, marasa galihu dukkaninsu sun amfana da shirin samar da lafiya.
Ya ce, a cikin shirin inganta sha'anin kiwon lafiya na kasar da zai shafi dukkan mazauna marasa hali cikin al'umma musammam ma 'yan kasar, da kuma bukatar ganin duk mazauna kasar Ghana sun samu wadataccen kula a fannin kiwon lafiya, shirin inshorar lafiyar zai yi rajistar mutane da dama a duk fadin kasar.