An bukaci Afrika da ta kebe kashi 15 cikin 100 na kasafin kudinta kan kiwon lafiya har zuwa shekarar 2015
Gwamnatocin kasashen nahiyar Afrika ya kamata su kebe kashi 15 cikin 100 bisa na kasafin kudinsu ga kiwon lafiya, in ji wani kwamitin shawara na Afrika na kungiyoyin addinai a ranar Alhamis, 17 ga wata. Babban mai fada a ji, kuma mamba na wannan kwamiti, Boniface Adoyo ya gayawa manema labarai a birnin Nairobi cewa karancin kudin da ake kashewa kan harkokin kiwon lafiyar jama'a ya kasance daya daga cikin matakan dake janyo karin adadin yawan mace macen mata da kananan yara a Afrika.
"Muna kiran gwamnatocin nahiyar Afrika da su girmama sanarwar Abuja ta shekarar 1999 dake bukatar a kalla a ware kashi 15 cikin 100 na kasafin kudin kasashen zuwa harkokin kiwon lafiya," in ji mista Adoyo a yayin wani taron kasa da kasa mai taken "imani domin rayuwa". (Maman Ada)