An dai samu halartar jami'an kasar Sudan, wakilan kwararrun likitoci na kasar Sin da ke aiki a kasar Sudan, da kuma dimbin mutanen da aka haife su a asibitin bisa taimakon kungiyoyin likitocin kasar Sin da suka fara aiki a can tun shekara ta 1972.
Mahjoub Mohamed, babban darektan asibitin Abu Ushar a cikin jawabinsa ya bayyana bikin da "kyaukyawar hulda ta fannin kiwon lafiya da ke akwai tsakanin kasar Sudan da ta Sin, musanman ma da asibitin Abu Usha". Ya yi kira da a kara bumkasa wannan hulda domin samun kwararru a wasu fanonin kiwon lafiya .
A cikin watan Yuni na shekara ta 2011, kasar Sudan da ta Sin sun gudanar da yarjejeniya domin tura kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya daga kasar Sin zuwa kasar Sudan domin gudanar da aiki na tsawon shekaru 2. A cikin wannan yarjejeniya kwararrun likitocin guda 37 daga kasar Sin za su taimakawa wajen masanyar fasaha da kimiyya da kuma kula da kayen aiki da kasar Sin ta ba kasar Sudan a asibitin Omdurman da kuma ta Abu Ushar a cikin jahar Gezira.(Abdou Halilou)