An nuna cewa, tsarin aikin farko na PRPSS ya samu tallafi daga kungiyar kasa da kasa kan cigaba ta IDA da bankin duniya, wanda ya tashi zuwa jimillar dalar Amurka miliyan 33,8, a ciki, miliyan 11 suka fito daga asusun gungun masu bada tallafin kudi. An fara wannan aiki a shekarar 2011 bisa muhimman manufofin bada taimako ga bunkasa samar da ayyukan kiwon lafiya masu inganci ga lafiya uwa da jinjirinta a kasar Benin, da karfafa karin aikin hukuma na ministan kiwon lafiya.
A cewar wannan kundi, karin taimakon da ya samu amincewa a ranar Alhamis na da burin tallafawa wajen aiwatar da tsarin samar da kulawar kyauta ga masu fama da zazzabin cizon sauro na IGPECP a cikin asibitocin kasar da aka fara tun cikin watan Oktoban shekarar 2011 zuwa ga mata masu juna biyu da kuma yara 'yan kasa da shekaru biyar da haihuwa.(Maman Ada)