Chen Zhu ya ce, za a bunkasa asibitocin gwamnatin kasar yadda ya kamata, domin a taimakawa kungiyoyi masu zaman kansu da su zuba jari wajen gina hukumomin kiwon lafiya. A nan gaba, za a fitar da manufofin amincewa da kungiyoyi masu zaman kansu su zuba jari a cikin gina hukumomin kiwon lafiya, da taimaka musu kan gina hukumomin bada jinya, da sa kaimi gare su da zuba jari kan bada hidimar kiwon lafiya ga kananan yara. Ban da wannan kuma, za a yi amfani da albarkatun kiwon lafiya a cikin asibitocin gwamnati da kuma na masu zaman kansu yadda ya kamata.
Ya zuwa yanzu, ana da hukumomin kiwon lafiya kimanin dubu 20 a kasar Sin, yawan hukumomi masu zaman kansu ya kai sulusi, amma gadajen dake cikin asibitoci masu zaman kansu da yawan mutane da suke zuwa asibitocin sun kai kashi 1 cikin kashi goma kawai. Bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsara, an ce, ya kamata yawan gadajen dake cikin asibitocin ya karu zuwa kashi 20 cikin kashi dari. (Zainab)