An isa da shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika a birnin Paris na kasar Faransa a ranar Asabar domin binciken lafiya bayan da kwanta rashin lafiya, a cewar kamfanin dillancin labarai na APS.
Bouteflika mai shekaru 76, zai tsaya birnin Paris domin samun jinya kamar yadda likitansa ya bukata, in ji wannan kafa.
Da yake rawaito kalaman darektan cibiyar asibitin wasannin motsa jiki ta kasa, forfesa Rachid Bougherbal, kamfanin dillancin labarai na APS ya bayyana cewa, shugaba Bouteflika ya samu wata matsalar jinin jiki a ranar Asabar da misalin karfe 12 da rabi bisa agogon wurin.
Matsalar rashin lafiyar shugaban kasar Aljeriya na cigaba da janyo hankalin kafofin watsa labarai da 'yan adawa na kasar tun yau da 'yan shekaru. Lamarin da ya sanya masu kai masa sara cewa, cikin wannan hali da yake, akwai wuya ya cigaba da mulki kasa balantana, har ma ya ce, zai yi takarar zaben shugaban kasa wa'adi na hudu a shekarar 2014. A 'yan shekarun baya bayan nan, shugaba Bouteflika ya rage tafiye-tafiyensa, musamman ma zuwa kasashen waje.
A shekarar 2005, Bouteflika ya samu jinya a asibitin Val-de-Grace dake birnin Paris na kasar Faransa, lamarin da ya janyo jita-jitar mutuwarsa.
Haka kuma, a cikin watan Satumban shakarar 2012, hukumomin kasar Aljeriya sun karyata wani sakamakon bincikin lafiya da kafofin kasar suka rawaito dake bayyana tsanancewar lafiyar shugaba Bouteflika. (Maman Ada)