in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 2 sun kamu da murar tsuntsaye a lardin Henan na kasar Sin
2013-04-14 16:18:07 cri
Hukumar lafiya ta lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin, ta sanar a ranar 14 ga wata cewa, an tabbatar da kamuwar mutane biyu, da cutar nan ta murar tsuntsaye nau'in H7N9, a wasu birane 2 na lardin. Wannan ya kasance karon farko da aka tabbatar da bullar wannan cuta a lardin na Henan.

Cikin wadannan mutane 2, daya ya kasance mai dafa abinci ne dake zaune a birnin Kaifeng, inda tuni aka sanya shi cikin wani dakin jinyar mutane da suka kamu da cututtuka masu tsanani. Shi kuwa dayan mutumin da ya kamu da cutar manomi ne daga birnin Zhoukou, kuma rahoton da aka samu ya nuna cewa tuni ya fara farfadowa, bayan kulawar jami'an lafiya da ya samu.

Ya zuwa yanzu dai, ba a gano wata alaka dake nuna dalilin kamuwar wadannan mutane biyu da cutar ta murar H7N9 ba. Tuni dai aka riga aka kebe mutane 19, wadanda ke zaune tare da su, domin yin bincike a kansu. Koda yake dai ya zuwa yanzu, ba a gano alamar kamuwar makusantan nasu da cutar ba.

Ban da haka, a ranar 14 ga wata a lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, an samu karin mutane 4 wadanda suka kamu da mutar tsuntsaye. Sakamakon haka, yanzu an sanar da kamuwar mutane 55 ke nan a dukkanin fadin kasar Sin, inda tuni 11 daga cikin su suka riga mu gidan gaskiya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China