in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar hada kan kasar Kenya ta yi kiran zaman lafiya
2013-03-21 10:31:36 cri

Hukumar hada kan kasar Kenya ta yi kira ranar Laraba, ga shugabannin siyasa a kasar, da su fifita zaman lafiya a kalamansu yayin da kasar ke jiran hukunci daga kotun kolin kasar, dangane da batun ingancin sakamakon zaben shugaban kasa.

Shugaban hukumar hadin kai ta kasar (NCIC) Mzalendo Kibunja ya bayyana wa 'yan jarida a birnin Nairobi cewa, ya dace zababben shugaban kasar Uhuru Kenyatta da firaminista Raila Odinga su yi la'akari da maganganu irin na siyasa dake fita daga bakinsu, su kuma jira sakamakon kara da ke kotu.

Shugaban ya ce, a kashin gaskiya an samu rabuwar kawuna a kasar Kenya tsakanin magoya bayan zababben shugaban kasar wadanda suka nuna gamsuwa kan sakamakon zaben, sannan su kuma masu goyon bayan firaministan ba su ji dadin yadda sakamakon zaben ya kasance ba.

Ya ce, da shi ke 'yan kasar Kenya suna jiran hukunci kan kara da aka shigar a kotun kolin kasar dangane da zaben, ya yi kira ga jama'ar kasar su zauna lafiya da juna.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China