Najeriya, wadda ta fi kowace kasa yawan al'umma a Afirka, ta samu babban ci gaba a fannin kiwon lafiya a wadannan shekaru, musamman ma a fannin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro wato malariya da kuma cutar sida, har ma jama'ar kasar na kara samun wayin kai game da ilimin kiwon lafiya. A albarkacin ranar 7 ga watan Afrilu na wannan shekara, da ta kasance ranar kiwon lafiya ta duniya karo na 63, wakilinmu Murtala yayi hira da shugaban kwamitin kula da harkokin kiwon lafiya a mataki na farko dake birnin Abuja, wato FCT Primary Health Care Board, Dr. Rilwanu Mohammed, dake kula da batun hawan jini, kiyaye lafiyar mata da yara, taka birki ga cututtuka masu yaduwa da sauransu.