in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

Rataya I

Shiri mai matakai takwas da Sin ta alkawarta a taron FOCAC na Beijing

1. Kara ba da taimako ga kasashen Afirka, wanda ya zuwa shekara ta 2009 taimakon da ta baiwa kasashen Afirka ya rubanya na shekara ta 2006.

2. Samar da bashin dala biliyan dubu uku da kuma rance ga masu sayen kayayyaki ga kasashen Afirka cikin shekaru uku na gaba

3. Kafa asusun samun bunkasa tsakanin Sin da Afirka, wanda sannu a hankali adadin kudinsa zai kai dalar Amurka biliyan biyar, dan karfafa gwiwar kamfunan kasar da suka zuba hannayen jari a Afirka da ba su goyon baya.

4. Tallafawa kungiyar tarayyar Afirka (AU) wajen gina tartibiyar cibiya, dan marawa yunkurin kasashen Afirka baya na tsayawa da kafafunsu ta hanyar hadin kai da gaggauta dunkulewa waje guda.

5. Yafe bashi maras ruwa na gwamnati wanda ya wajaba a biya kasar Sin a karshen shekara ta 2005 ga matalautan kasashe dake fama da kangin bashi da kasashe koma baya a Afirka da suke da huldar diflomasiyya da Sin.

6. Kara bude kasuwar Sin a Afirka, da kara adadin kayayyakin fito na Afirka zuwa Sin ba tare da biyan haraji ba daga 190 zuwa 440, na kasashen dake da dangantakar diflomasiyya da Sin.

7. Kafa shiyyoyin kula da tattalin arziki da cinikayya uku zuwa biyar a kasashen Afirka nan da shekaru uku.

8. Horas da ma'aikata dubu 15 nan da shekaru uku dan kasashen Afirka, tura manyan kwararru a fannin ayyukan gona ga Afirka, kafa cibiyoyin nune-nunen fasahohin ayyukan gona guda 10 masu sigogin musamman a Afirka, taimakawa kasashen Afirka wajen gina asibitoci 30 da samar da kyautar kudin Sin yuan miliyan 300 ga kasashen Afirka , dan yin amfani da shi wajen sayen magungunan hana zazzabin cizon sauro kamar artimisinin, da gina cibiyoyin kare da magance zazzabin cizon sauro, tura ma'akatan sa kai matasa 300 zuwa kasashen Afirka, tallafawa kasashen Afirka wajen gina makarantu 100 a yankunan karkara, kara adadin daliban Afirka da gwamnatin kasar Sin zata dauki nauyin karatunsu daga dubu biyu a shekara zuwa dubu hudu a shekara daga karshen shekata ta 2008.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China