in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

III. Bayar da muhimmanci da samar da kayayyakin more rayuwa

Koma baya ta fuskar kayayyakin more rayuwa ita ce babbar matsalar da ke kawo karan tsaye ga ci gaban galibin kasashen Afirka,samar da irin wadannan kayayyaki yana daya daga cikin muhimmin bangaren hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Afirka. Sin tana bayar da muhimmanci sosai wajen taimakawa kasashen Afirka su inganta kayayyakinsu na more rayuwa ta hanyar taimaka musu wajen gina gidajen kwana, hanyoyi,gadoji, layin dogo, filayen saukar jiragen sama, tashoshin jiragen ruwa, sadarwa, tashoshin samar da wutar lantarki, ruwan sha, magudanun ruwa, asibitoci ko ta hanyar kwangila ko kuma ta hanyar zuba jari cikin hadin gwiwa da fadada hanyoyin bayar da tallafi kuma sun yi tasiri ga ci gaban Afirka.Sin tana karfafawa kamfanoninta gwiwa da su gudanar da ayyuka masu inganci kuma bisa yarjejeniyar kwangilolin da aka cimma kana su kare mutuncin sunan da suka yi.

A 'yan shekarun baya Sin ta taimakawa kasashen Afirka wajen gina ayyukan more rayuwa da dama. A shekarun 1970 duk da matsalar tattalin arzikin da ta fuskanta, Sin ta taimaka wajen gina layin dogo mai nisan kilomita 1860 daga Tanzania zuwa Zambia wanda ya kasance aikin tallafin kashi kai na tarihi da Sin ta baiwa Afirka.

Cibiyar taron kasa da kasa da ke Alkahira da Sin ta taimaka aka gina ya kai fadin murabba'in kilomita 58,00 kuma ana gudanar da sama da taruka da nune-nune na kasa da kasa guda 100 a kowa ce shekara a cikinsa wannan ya taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci da yawon shakatawa. Ya zuwa karshen shekarar 2009 Sin ta samar da tallafi wajen gina ayyukan kayyakin more rayuwa sama da 500 a Afirka, sauran manyan ayyukan da ta samar sun hada da tagwayen hanyoyin Belet Uen-Burao a Samoliya, tashar jirgin ruwan Harbor da ke Mauritania, mashigin tekun mashta al Anad-Ben jarw a Tunisa, babban filin wasa na kasa a Tanzania, cibiyar gudanar da babban taron kungiyar AU da sauran ayyaukan da ake gudanarwa a halin yanzu.

Gwamnatin Kasar Sin ta yi tayin samar da rance dabam-dabam a kokarin da ta ke na taimakawa kakashen Afirka su inganta kayayyakinsu na more rayuwa. Kana ta goyi bayan hukumominta na kudi da su kara yawan rancen kasuwancin da suke baiwa Afirka. Tun lokacin da aka kafa dandalin FOCAC, Sin ke tsayawa tsayin daka wajen tallafawa Afirka. Daga shekarar 2007 zuwa shekarar, 2009 Sin ta samar da rance da tallafin kudi da ya kai dala biliyan 5 ga masu fitar da kayayyaki zuwa Afirka. Har ila ta yi alkawarin samarwa Afirka rancen da ya kai na dala biliyan 10 daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2012. Kuma za a yi amfani da wadannan rance ne wajen tafiyar da wasu manyan ayyuka da ake gudanarwa, kamar filin jirgin sama a Mauritius, gidajen kwana a Malabo da Equatorial Guinea da kuma tashar samar da wutar lantarki mai amfani da karfin ruwa a Bui da ke kasar Ghana.

Kamar yadda dokokin kasa da kasa suka shimfida, kamfanonin Sin sun gudanar da kwangiloli a Afirka ta hanyar shiga takarar neman kwangiloli kuma sun taimaka wajen gina kayayyakin more rayuwa masu inganci kuma cikin rahusa. Irin wadannan kayayyaki sun hada da gidajen kwana,hanyoyi, filin jiragen sama, matatun mai, tashoshin sadarwa, tashoshin samar da wutar lantarki masu amfani da karfin ruwa wadanda aka fadada su da fasahohin zamani. Kamfanonin Sin sun nuna karfinsu a Afirka lokacin da suke shiga takarar neman kwangila su kadai ko ta hanyar yin hadin gwiwa da 'yan kasuwan kasa da kasa kuma sun bunkasa kwarewarsu a harkokin gudanarwa ta kasa yayin da suke kara samun kwarewa ko ilimi da samar da kwararrun mutane.Sin ta tallafa wajen samar da ayyuka da dama wadanda tuni aka kammala su, wadannan sun hada da otel din Sheraton da aka gina a Algeria, tashar sadarwa a Habasha, layin dogo a Libya da fitilun layin dogo a Lagos Najeriya.

Kamfanonin Sin suna gudanar da ayyukan inganta jin dadin rayuwar jama'a kamar yadda aka tsara, kuma suna shiga shirye-shiryen da zasu amfanawa alummomin da suke gudanar da ayyukansu a wajen, wannan mataki ya samu yabo sosai daga hukumomi da jama'ar wurin.Sin ta samar da tallafin kudade wajen gina hanyoyi, gadoji, asibitoci da makarantu da tona rijiyoyi. Bugu da kari kamfanonin sun bayar da gudummawar kayayyaki wadanda za su yi tasiri ga ci gaban al'ummomin da ke karkara.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China