in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA

OFISHIN WATSA LABARAI NA MAJALISAR GUDANARWA NA KASAR SIN

Disamba, 2010

Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kuma Afirka ta kasance gida ga galibin kasashe masu tasowa. Yawan al'ummomin kasashen Sin da Afirka ya zarce daya bisa biyu na yawan al'ummomin duniya, kuma batun bunkasa tattalin arziki da jin dadin rayuwar jama'a shi ne muhimmin abin da Sin da Afirka suke mayar da hankali a kai.

A shekarun da suke kokarin neman ci gaba, Sin da Afirka sun taka muhimmiyar rawa wajen ba da gudumawa ga ci gaban albarkatu da tattalin azikin juna, ta hanyar mutunta tare da ci gaba da bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya don moriyar juna da bunkasuwa tare. Abubuwa a zahiri sun tabbatar da cewa, hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka ta dace da moriyar bangarorin biyu kuma ta taimakawa Afirka wajen cimma nasarar muradun karni na MDD da bunkasa makoma da ci gaban Sin da Afirka.

A shekarun 1950 hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka ta mai da hankali ne kan cinikayya tsakanin bangarorin biyu da taimakon da Sin ke baiwa Afirka. Hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu ta bunkasa daga dukkan fannoni kuma ana kara samun sakamako mai kyau. Musamman tun lokacin da aka kafa dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2000 hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka take kara farfadowa da bunkasuwa, sannan an samu ci gaba a fannonin cinikayya, zuba jari, kayayyakin more rayuwa da manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, bugu da kari an kara fadada hadin gwiwa ta fuskar tallafi da yawon shakatawa abin da ya kai ga samun hadin gwiwa a fannoni da dama da ya kai wani sabon matsayi a tarihi.

Hadin gwiwar Sin da Afirka wani muhimmin mataki ne na dangantakar 'yan uwantaka, kuma ya haifar da wata sabuwar rayuwa ga Nahiyar, kana ya daga darajar matsayin siyasa da tattalin arzikin kasashe masu tasowa a duniya, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen yayata kafa tsarin nuna adalci a sabuwar dokar siyasa da tattalin arzikin duniya, Sin na son yin mu'amala tare da sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa don karfafa tuntubar juna da hada kai da kasashen Afirka, shiga a dama da ita wajen gina Afirka, hada kai wajen shimfida zaman lafiya da ci gaba a Afirka.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China