in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

Kammalawa

Duniya a yau tana fuskantar manyan sauye-sauye da wasu matakan ci gaba. Koma bayan tattalin arzikin da ta abku sakamakon rikicin hada-hadar kudi na kasa da kasa, ba ta kare ba tukuna. Batutuwan da suka shafi duniya kamar kariyar abinci, samar da makamashi, sauyin yanayi da kare gami da shawo kan cutuka masu yaduwa sun zamo bayyanannu. Kana ga karuwar lamura na rashin tabbas a yanayin tattalin arzikin duniya. A matsayinsu na masu tasowa Sin da kasashen Afirka yanzu suna fuskantar damar kyautata yanayin habakarsu da ma irin kalubalolin dake tattare da matsalolin duniya.

Sin da Afirka suna amfanar juna. Bukatunsu na karuwa akai-akai, kana makomar hadin gwiwarsu ta tattalin arziki da cinikayya tana da haske. Bisa akidar nuna daidaito, samun moriyar juna da bunkasuwa, Sin zata ci gaba da aiwatar da matakan jawo musayar tattalin arziki ta fuskar tsare-tsaren da zasu shafi sassa biyu ko fiye a hadin gwiwarta da Afirka, fadada bigiren yin hadin gwiwa, gano sabbin dabarun yin hadin gwiwa da raba alfanun samun bunkasa da kasashen Afirka.

Yayin da ake ci gaba da tafiyar da tsarin tattalin arziki na bai daya a duniya, tabbas hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka zai samu zarafin tabo sassa da dama, ya fadada tare da bunkasa, sakamakon muhimmancin da zasu bashi, wanda ka iya samar da sabon kuzari da zama ga baki dayan hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka tare da tallafawa wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya, ci gaba da lumana a duniya.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China