in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

Rataya II

Sabon shiri mai matakai takwas da Sin alkawarta a taron ministocin FOCAC karo na hudu.

1. Sin ta shirya kulla kawance tsakaninta da Afirka game da batun shawo sauyin yanayi da tuntubar juna tsakanin manyan jami'ai a lokaci-lokaci dan karfafa hadin gwiwa a fannin kula da yanayi ta tauraron bil Adama, bunkasa da yin amfani da sabon makamashi, magancewa da shawo kan kwararowar Hamada da kuma kare muhallin birane.Gwamnatin kasar Sin ta yanke shawarar tallafawa kasashen Afirka da wasu ayyukan samar da makamashi mai tsabta guda 100, ta hanyar amfani da hasken rana, takin gargajiya da 'yan kananan tasoshin samar da wutar lantarki ta amfani da ruwa.

2. Kyautata hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha. Sin ta tsara kaddamar da shirin kawance tsakaninta da Afirka ta fannin kimiyya da fasaha, gudanar da ayyukan nune-nune guda 100 kan ayyukan bincike na hadin gwiwa, gayyatar dalibai 100 na Afirka da suke karatu a fannin zama manyan likitoci dan gudanar da bincike a kasar Sin tare da muradin tallafa musu yayin da suka koma kasashensu dan yin aiki.

3. A kokarin karawa kasashen Afirka karfi ta fannin harkokin kudi, gwamnatin kasar Sin zata samar musu da bashin dalar Amurka biliyan 10. Sin tana marawa bullo da shirin ba da bashin musamman na dalar Amurka biliyan daya da cibiyoyin kudi na kasar suka yi, dan bunkasa harkokin kanana da matsakaitan masana'antu a Afirka. Gwamnatin Sin zata yafewa kasashen dake fama da kangin bashi da wadanda suke koma baya a Afirka, masu dangantakar diflomasiyya da Sin bashin da ta basu, wanda ya wajaba su biya a karshen shekara ta 2009.

4. Sin zata bude kasuwarta a kasashen Afirka. Sannu a hankali Sin zata baiwa kasashe mafiya koma baya na Afirka masu dangantakar diflomasiyya da ita dammar shigar da kayan das u kan samar na kashi 95 ba tare da biyan haraji ba. A matakin farko, Sin ta aiwatar da irin wannan kuduri a shekara ta 2010 da kashi 60 ga kayan fito na irin wadannan kasashe.

5. Domin ci gaba da karfafa hadin gwiwa a fannin ayyukan gona da bunkasa kokarin kasashen Afirka na samar da kariyar abinci, Sin zata kara adadin cibiyoyin nune-nunen fasahar ayyukan da ta kakkafa a kasashen Afirka zuwa 20, tura tawagogin samar da fasahohin ayyukan gona 50 zuwa Afirka tare da taimakawa wajen bayar da horo ga malaman gona 2,000 a Afirka.

6. Sin zata ci gaba da zurfafa hadin gwiwarta da Afirka a harkar kiwon lafiya. Zata samar da kayan kiwon lafiya na kudin kasar yuan miliyan 500, da kayan yakar zazzabin cizon sauro ga asibitoci 30 da cibiyoyin bayar da kariya da magance zazzabin cizon sauron, wadanda aka samar da tallafin kasar ta Sin, da kuma taimakawa wajen horas da adadin likitoci da ma'aikatan jinya na kasashen Afirka dubu uku.

7. Domin tabbatar da hadin gwiwar ta fuskar bunkasa harkokin jama'a da na ilimi, gwamnatin kasar Sin zata taimakawa kasashen Afirka wajen gina makarantu 50 na abota tsakanin Sin da Afirka, tare da horas shugabanni da malaman makarantu 1,500, kara adadin daliban Afirka da gwamnatin kasar Sin zata dauki nauyin karatunsu zuwa 5,500 nan da shekara ta 2012, da horas da ma'aikata a sassa daban-daban na kasashen Afirka nan da shekaru uku masu zuwa.

8. Dan fadada musaya a tsanin mutane, Sin ta aiwatar da shirin hadin gwiwa kan ayyukan bincike da yin musaya da nufin karfafa hadin gwiwa da yin musaya a tsakanin manyan malamai da masu lura da al'amuran da ka je su zo, lamarin da zai samar da goyon baya ta fuskar basira dan inganta hanyoyin tsara manufofi kan hadin gwiwar sassan biyu.     Tamat


1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China