in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

II. Fadada Bangaren Zuba Jari

Sin ta fara zuba jari ne a Afirka a shekarun 1980 a bangaren kananan masana'antu. Kana a shekarun 1990 Sin ta ci gaba da fafada harkoki da matakanta na zuba jari a Afirka. Tun a shekarar 2000, karkashin shirin nan na FOCAC harkokin zuba jarin Sin sun ci gaba da bunkasa, A halin da ake ciki kuma, ita ma Afirka ta yunkuro a harkarta ta zuba jari a Sin kuma kasuwar kayayyakin Afirka na ci gaba da samun karbuwa a kasuwar Sin.

A 'yan shekarun nan, jarin da Sin ta ke zubawa a Afirka ya kai wani sabon matsayi. Da farko ya bunkasa cikin hanzari, ya zuwa karshen shekarar 2003 jimillar kudin jarin da Sin ta zuba kai tsaye a Afirka ya kai dala miliyan 490, inda ya karu zuwa dala biliyan 9.33 a karshen shekarar 2009. Na biyu kasashen da Sin ta zuba jari a cikinsu: Kasar Sin ta zuba jari a kasashen Afirka 49, kuma ya fi yawa a Afirka ta kudu, Najeriya, Zambia, Sudan, Algeria, Masar. Na uku, Sassan da Sin ta zuba jari a Afirka sun hada da hako ma'adinai, bayar da tallafi, Masana'antu, gine-gine, yawon shakatawa, aikin gona, gandun daji, kiwon dabbobi da kiwon kifaye. Na hudu, hanyoyin zuba jari: baya ga zuba jari kai tsaye da kuma hadin gwiwa, har ila an fadada hanyoyin zuba jari kamar ba da zarafi ga juna da hadin gwiwa da wasu kamfanoni ko mallakar kamfanonin da yin hadin gwiwa da kamfanonin kasashen don bunkasa albarkatu. Na biyar, masu zuba jari dabam-dabam: manya da matsakaitan masana'antun kasashen da masana'antu masu zaman kansu da daidaikun jama'a sun zuba jari tare da fara harkokinsu a Afirka inda suke tallafawa juna ta hanyoyi dabam-dabam.

Gwamnatin kasar Sin tana karfafa gwiwa tare da taimakawa kamfanoni Sin masu karfi kuma wadanda suka yi suna da su fadada harkokinsu a Afirka, kuma Sin ta dauki matakan da suka dace don yi musu jagora a wannan fanni kuma hakan ya haifar da sakamako mai kyau. Da farko an samar da yanayin zuba jarin da ya dace ta hanyar sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi da daukar wasu matakai. Ya zuwa yanzu Sin ta sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi da daukar wasu matakai. Inda ta sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi da kasashen Afirka 33 a fannonin bunkasa da kuma kare sha'anin zuba jari, kana ta sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi da wasu kasashen Afirka 11 don ganin ba su biya haraji sau biyu 2 ba, al'amarin da ya haifar da kyakkyawan yanayin hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da Afirka. Na biyu, Sin ta bude asusun raya Sin da Afirka, wannan wani asusu ne da zai amfanawa juna da kungiyoyin kudi na Sin suka bullo da shi don ba da tallafi na musamman ga kamfanoni da 'yan kasuwan sin yayin da suke zuba jari a Afirka. Tun lokacin da aka kafa asusun shekaru 3 da suka gabata, asusun ya zuba jari a sama da ayyuka 30 wadanda suka hada da sashen raya aikin gona, samar da injunan masana'antu, wutar lantarki, kayayyakin gine-gine, yankunan masana'antu, hako ma'adinai, tashoshin jiragen ruwa da dai sauransu. Ya zuwa yanzu an kammala matakin farko na asusun na dala biliyan 1 kuma ana saran asusun zai tara kudin da ya kai dala biliyan 5. Na uku, Sin na kokarin ganin an gina shiyar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a Afirka, al'amarin da ya samu goyon bayan gwamnatocin sassan biyu, kuma kamfanonin Sin suke sa-ido kan gina kayayyakin more rayuwa a wadannan shiyoyi, wannan ya taimaka wajen jawo hankalin Sinawa da kamfanonin ketare har ma sannu a hankali suna kulla yarjejeniyar kafa masana'antu. A halin yanzu Sin tana gina shiyoyin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya guda 6 a kasashen Zambia, Mauritius, Najeriya, Masar, Habasha baya ga jarin dala miliyan 250 da ta zuba a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa.

Shiyyar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Zambia da Sin ita ce ta farko da Sin ta kaddamar a ketare. Ya zuwa yanzu kimanin kamfanoni 13 sun kaura ciki, inda suke gudanar da ayyukan da suka shafi hako ma'adinai, bincike, sarrafa karafa, hada sinadarai, gine-gine, sannan ta zuba jarin da ya kai dala miliyan 600 da samar da guraben aikin yi sama da dubu 6 ga mazauna wurin.

Allah ya albarkaci kasashen Afirka da albarkatu, don haka hadin gwiwa a bangaren bunkasa albarkatu wani muhimmin bangare ne na hadin gwiwar zuba jari tsakanin Sin da Afirka. A 'yan shekarun nan bisa akidar hadin gwiwar moriyar juna da ci gaba tare kamfanonin Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa albarkatun Afirka, kana suna taimakawa kasashen Afirka su bunkasa masana'antun dake sarrafa albarkatu ta yadda za su inganta albarkatunsu, ta hanyar amfani da albarkatun wajen inganta jin dadin rayuwa da raya tattalin arziki.yayin da suke yin hadin gwiwa kamfanonin Sin suna bin dokokin da aka amince da su a duniya sau da kafa, bude kofa, nuna gaskiya da adalci, amfani da matakan hadin gwiwa dabam-dabam ta yadda za su hako tare da amfana da albarkatun tare da kasahen Afirka har ma da kamfanonin kasa da kasa kuma sun yi Allah wadai da nuna babakere da wariya.

Jarin da kamfanonin Sin suka zuba a wannan fannin ya kara yawan kudaden shigan Afirka, daga darajar irin wadannan albarkatu, taimakawa wajen gina ayyukan more rayuwa, bunkasa tattalin arziki, wannan ya samu goyon bayan hukumomi da na jama'a. Alal misali, kamfanonin kasashen Sin da ke kasar Malaysia sun hada gwiwa da kasar Sudan ta fuskar hako mai kuma ya taimakawa kasar wajen gina matatar mai na zamani inda ake hako mai a doron kasa da cikin teku, al'amarin da ya kara yawan kudin shigar da Sudan take samu kana ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwar al'ummomin da ke yankunan karkara.

Kamfanonin kasar Sin da ke gudanar da harkokinsu a Afirka suna ba da kulawa ta musamman ga kyakkyawar dangantaka tsakaninsu da alummomin da suke aiki a wurin ta hanyar aiki da dokokin da aka gindaya, kare mutuncinsu, kyautata muhallin albarkatu da kare muhalli.kana suna daukar mutane aiki tare da kara karfin kasashen Afirka ta yadda za su ci gaba ba tare da neman taimako daga waje ba. Wannan ya taimaka matuka ga ci gaban tattalin arzikin Afirka yayin da suke kokarin kara ci gabansu.Alal misali wani kamfanin hako ma'adinai da ke kasar Zambia ya zuba jari inda ya kafa wasu masana'antun sarrafa albarkatun Tagulla. Bayan abkuwar matsalar hada-hadar kudi ta duniya, kamfanin ya yi alkawarin cewa ba zai rage yawan kayayyakin da ya ke samarwa, ko dakatar da aikinsa ba, sannan ba zai rage yawan jarinsa ba,wannan shi ne kamfani daya tilo da bai rage yawan kayayyakin da ya ke samawar ko ma'aikata daga cikin kamfanonin waje 7 da suka zuba jari a bangaren hako ma'adinai a kasar Zambia ba.

A 'yan shekarun nan, yayin da tattalin arzikin Afirka ke bunkasa kana kasuwannin Sin suka ci gaba da kara girma, kasashen Afirka na ci gaba da kara zuba jari a Sin. Kasashen Afirka ta kudu, Seychelles, Najeriya da Tunusia su ne kasashen Afirka da ke kan gaba wajen zuba jari a Sin. Wata barasa da wani kamfanin kasar Afirka ta kudu ya fara samarwa cikin hadin gwiwa a Sin a halin yanzu yana tafiyar da wasu kamfanonin barasa kusan 70. Sannan akwai wani kamfanin takin zamani da ya yi suna a Sin wanda na hadin gwiwa ne da aka kafa tsakanin kamfanin kasar Tunisia da na Sin. A karshen shekarar 2009 kudin jarin da kasashen Afirka suka zuba kai tsaye a Sin ya kai dala biliyan 9.93, wannan ya shafi bangarorin albarkatu, manpetur, Injuna, kayayyakin lantarki, sufuri, sadarwa, kananan masana'antu, kayayyakin amfanin gona, tufafi, maganguna, bunkasa sha'anin aikin gona, nishadantarwa, gidajen kwana da dai sauransu. Jarin da Afirka ta zuba a Sin ya dace da moriyar juna, al'amarin da ya bunkasa sha'anin fitar da kayayyakin Sin zuwa Afirka da sauran shiyoyin duniya.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China