in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

V. Tallafi dan bunkasa zaman rayuwar jama'a

Idan Afirka na son cimma burin muradun karni, wajibi ne ta bunkasa kayan amfanin jama'a, shawo kan matsalolin karancin abinci, kyautata yanayin tsafta da rage kangin bashin waje. Sin tana nuna matukar kulawa kan yanayin rayuwar al'umar Afirka, tare da tallafawa kasashen Afirka wajen gina kayan amfanin jama'a, habaka hanyoyinsu na samar da kayan amfanin gona, bunkasa matakansu na kula da lafiyar jama'a, kana a aikace ta rage musu bashin dake kansu, sannan tana samar da tallafi a gare su game da abkuwar bala'u da ma na jin kai.

Zagewa wajen ba da taimakon gina kayan more rayuwar jama'a. Sin ta baiwa kasashen Afirka tallafi, wajen gudanar da ayyukan samarwa jama'a kayan walwala masu yawa, kamar su gidaje masu saukin kudi, haka rijiyoyi dan samar da ruwa, sarrafa shara, kyautata tsarin yada labarai ta rediyo da talabijin da ma harkar sadarwa, taka muhimmiyar rawa dan bunkasa yanayin zaman rayuwar al'ummun waje. Misali, ayyukan samar da gidaje masu saukin kudi a Seychelles, Mozambique, Angola da Habasha sun kyautatayanayin zaman al'ummun wuraren. Ayyukan haka rijiyoyi a Najeriya, Senegal da Equatorial Guinea, da kafa tsarin hanyoyin samar da ruwa a Tanzaniya da Jamhuriyar Nijar sun taimaka wajen shawo kan matsalar ruwan sha ga mutane da dama. Cibiyar watsa shirye-shiryen talabijin a Equatorial Guinea kuwa ta tabbatar da yiwuwar gudanar da ayyukan kafofin talabijin na kasar.

Gudanar da hadin kai a sassan ayyukan gona. Kariyar abinci na da muhimmanci ta fuskar dorewar ci gaba da tafiyar da yunkurin saukaka fatara a Afika.Ga mafi yawan kasashen Afirka aikin gona shi ne tushe, kuma shi ne sashin da aka fi baiwa muhimmanci a kokarin tafiyar da hadin gwiwar Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da cinikayya. A koda yaushe Sin na daukar tallafawa Afirka wajen shawo kan matsalar kariyar abinci a matsayin muradinta na hakika a hadin gwiwarta da Afirka ta fannin ayyukan gona. Muhimman sassan yin hadin gwiwar ayyukan gona tsakanin Sin da Afirka sun hada da samar da gine-gine, sarrafa kayan abinci, renon halittu, musayar fasahohin ayyukan gona, sai kuma sarrafawa, adanawa da yin safarar kayan amfanin gona. Ya zuwa shekara ta 2009, Sin ta taimaka wajen kafa wasu ayyukan gona sama da 142 a Afirka, kamar samar da tasoshin fasahar ayyukan gona na farko, tasoshin baza fasahohin ayyukan gona da ma gonakin. Sin ta kaddamar da cibiyoyin yada fasahohin aikin gona a Afirka, tare da samar da kayan gudanar da ayyukan gona da yawa. Kaza lika gwamnatin kasar Sin ta baiwa kamfanoninta kwarin gwiwar zuba jari a fannin sarrafa kayan amfanin gona da gudanar da ayyukan bunkasa aikin gona a Afirka.

Kyautata yanayin kiwon lafiya a Afirka. Manyan matakan da Sin ta dauka dan tallafawa kasashen Afirka su habaka yanayin kiwon lafiya sun kunshi, ta yin taimakon gina asibitoci, tura tawagogin kiwon lafiya zuwa Afirka, da samar da magunguna. Ya zuwa karshen shekara ta 2009, Sin ta taimaka wajen giggina asibitoci 54, kafa cibiyoyin kariya da magance cutar zazzabin cizon sauro guda 30, gami da samar da magungunan kawar da zazzabin cizon sauro na kimanin kudin Sin yuan miliyan 200 ga kasashen Afirka 35. Tun shekarar 1963, Sin ta tura ma'aikatan kiwon lafiya da yawansu ya kai dubu 18, zuwa kasashe 46 na Afirka, inda suka duba lafiyar kimanin majinyata miliyan 200 tare da horas da dubun dubatar ma'aikata a fannin kiwon lafiya a Afirka, cikin goman shekaru. Ba kawai wadannan ma'aikatan kiwon lafiya sun taimaka wajen samun waraka daga cuce-cucen da aka saba gani yau da kullun ba, har ma sun samar da wani yanayi na yin ayyukan masu cike da kalubale, kamar su kula da masu fama da yoyon fitsari da sankarau, sake mayar da wasu sassan jiki da fitar da manyan kari, kokarin ceto rayukan majinyata da dama da suka kasance cikin hadari da ma cike gurabu a kasashen da suke taimakawa. A halin yanzu, fiye da Sinawa ma'aikatan kiwon lafiya dubu daya ne suke gudanar da ayyuka kiwon lafiya daban-daban a kasashen Afirka 41.

Rage bashin dake kan Afirka. A ko da yaushe gwamnatin Sin na marawa kasashen Afirka baya, a kokarinsu na rage bashin dake kansu, da taimaka musu wajen rage nauyin bashinta dake kansu. Daga shekara ta 2000 zuwa ta 2009, Sin ta yafe nau'o'in bashi 312 ga wasu kasashen Afirka 35, wadanda adadinsu ya kai na kudin Sin yuan biliyan 18.96. Wadannan irin matakan saukaka bashi da aka bayyana, suna nuna kudurin Sin da muradinta na son taimakawa Afirka ta bunkasa, tare da jawo hanzarin matakan wasu kasashe na ragewa Afirka bashin.

Zagewa wajen saukaka bala'u da ba da tallafin jin kai. A aikace, Sin da Afirka sun gudanar da musayar ma'aikatan saukaka da rage abkuwar bala'u, da bunkasa hadin gwiwa gami da musayar ra'ayoyi. Yayin da bala'u ko yaki suka abku a wasu kasashen Afirka, ba tare da wata-wata ba Sin take yi musu tayin agajin jin kai. Yayin da take kara samun karfi, Sin ta kara matsayin agajin jin kai ga Afirka. A shekara ta 2003, yayin da kasar Aljeriya ta gamu da girgizar kasa mai karfin digiri 6.8, nan take Sin ta tura kayan tallafin da kudinsu ya kai dala miliyan 5.36, tare da tura tawagar ceto a gurin da bala'in ya abku.

A shekara ta 2004, a hukumance Sin ta kafa wani tsarin ba da agajin gaggawa a fannin saukaka bala'u, wanda ya taimaka wajen hanzarta aikin samar da sauki kuma mai inganci. A 'yan shekarun nan, Sin ta samar da kayan tallafin gaggawa irin su abinci da tantuna ga kasashen Sudan, Madagascar, Burundi, Tanzania, Somaliya, Habasha, Lesotho da Zimbabwe, inda ta taimakawa wadannan kasashe wajen habaka kokarinsu na samun kariya daga bala'u, da sake gina kansu bayan abkuwar bala'un. Tun daga shekara ta 2004, Sin ta baiwa kasar Sudan kyautar kusan kudin kasar yuan miliyan 150 dan samar kayan jin kai, haka rijiyoyi da ayyukan samar da ruwa a Darfur.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China