in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

I. Yayata ci gaban cinikayya

Batun cinikayya shi ne matakin farko na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, yayin da Sin ta bunkasa hadin gwiwar ta da Afirka da samun karuwar musaya tsakanin Sin da Kasashen Afirka, haka ma cinikayayya tsakanin sassan biyu ya kara fadada. Yawan kudin cinikayya tsakanin Sin da Afirka ya kai dala miliyan 12.14 ne kawai a 1950, amma ya karu zuwa dala miliyan 100 a shekarar 1960, kana ta zarce dala biliyan 1 a shekarar 1980. Bayan da adadin ya kai matsayin dala biliyan 10 a shekarar 2000, hadin gwiwar cinikayya tsakanin Sin da Afirka ya ci gaba da bunkasa fiye da yadda aka zata. A shekarar 2008 yawan kudin cinikayya tsakanin Sin da Afirka ya zarce dala biliyan 100, sannan yawan kudin kayayyakin da Sin ta fitar zuwa Afirka ya kai dala biliyan 50.8 kana kudin kayayyakin da aka shigo da su Sin daga Afirka ya kai dala biliyan 56. Matsakaicin karuwar kudin cinikayya a shekara tsakanin Sin da Afirka tsakanin shekarar 2000 shekarar 2008 ya kai kashi 33.5 cikin 100, kudin cinikayyar ketaran Sin ya tashi daga kashi 2.2 zuwa kashi 4.2 cikin 100, kana rarar kudin cinikayyarta da Afirka ya karu daga kashi 3.8 zuwa kashi 10.4 cikin 100. Ko da ya ke yawan kudin ciniki tsakanin Sin da Afirka ya ragu zuwa dala biliyan 91.07 a shekarar 2009 sakamakon matsalar hada-hadar kudi ta duniya, amma Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayyar Afirka a shekarar a karon farko. Yayin da tattalin arzikin duniya ke farfadawo, haka ma cinikayya tsakanin Sin da Afirka ke ci gaba da farfadawo da bunkasa. Daga watan Janairu zuwa Nuwanban shekarar 2010, yawan kudin ciniki tsakanin Sin da Afirka ya kai dala biliyan 114.81, inda ya karu da kashi 43.5 cikin 100 a kowa ce shekara, wato ya karu da kashi 43.5 cikin kashi 100.

Sakamakon bunkasuwar yanayin cinikayya tsakanin sassan biyu, ya sa kayayyakin kasashen ke shiga kasuwannin juna ba tare da wata matsala ba.

A shekarun 1980 da kuma 1990, kasar Sin na fitar da kayayyakin da ba su da nasaba da masana'antu zuwa Afirka kamar abinci, sinadarai, kayayyakin gargajiya da fatun dabbobi. Tun daga shekarar 2000 kayayyakin masana'antu da na wutar lantarki da Sin ke fitarwa zuwa Afirka suka karu, inda aka kara ingancinsu da fasahohinsu a kasuwanni. A halin yanzu jimillar yawan injuna da kayayyaki masu amfani da wutar lantarki da Sin ke fitarwa zuwa Afirka ya zarce rabi. Auduga da sinadarin phosphate suna daga cikin abubuwan da Afirka ke fitarwa zuwa Sin. A shekarun nan kayayyaki irinsu tama, gorar-ruwa, sinadarin hada takin zamani da kayayyakin wutar lantarki da ake samarwa a Afirka sun samu nasarar shiga kasuwannin Sin. Bugu da kari kayayyakin aikin gona da Afirka ke fitarwa zuwa Sin sun kara karuwa.

Kayayyakin da suka yi suna a cikin gidan kasashen Afirka kamar wani nau'in Lemo daga kasar Masar, Barasa daga Afirka ta kudu, Cocoa daga Ghana, Coffee daga Uganda, Man-zaitun daga Tunisia, Sesame daga Habasha dukkansu sun samu karbuwa a tsakanin Sinawa. Sanadiyar tasirin matsalar hada-hadar kudi ta duniya, kayayyakin da ke shigowa Sin daga Afirka sun ragu a shekarar 2009, amma kayayyakin gona da ake shigo da su son karu da kashi 25 cikin 100.

Sakamakon akidar nan ta cin moriyar juna, Sin ta shafe shekaru da dama tana bunkasa hadin gwiwar cinikayya yadda ya kamata tsakaninta da Afirka. Kasar Sin ta kulla yarjejeniyar cinikayya da kasashen Afirka 45 kana ta bunkasa hadin gwiwa ta fannonin aikin kwastan, haraji, sa-ido da ba da tallafi a kokarin samar da kyakkyawan yanayi ga ci gaban hadin gwiwar cinikayya tsakaninta da Afirka.

A kokarin ganin an fadada matakan da Afirka ke amfani da su wajen fitar da kayayyaki zuwa Sin, ya sa kasar Sin ta dauke wa kasashen Afirka marasa karfin ci gaba wadanda suka kulla huldar diplomaasiya a tsakaninsu biyan haraji kan wasu kayayyakin da suke shigarwa zuwa Sin tun a shekarar 2005. Ya zuwa watan Yulin shekarar 2010 yawan irin wadannan kayayyaki da ba a biya musu haraji sun karu zuwa 4700, kuma ana saran su kai kashi 95 cikin 100 na yawan kayayyakin dake jerin kayayyakin da ake biya musu haraji a dokokin kasar Sin dangane da harajin shigi da fici. Godiya ga wannan tsari, kuma ya taimaka matuka ga kayayyakin da Afirka ke fitarwa zuwa kasar Sin da ba a biya musu haraji sai karuwa suke.

Daga shekarar 2005 zuwa karshen watan Yunin shekarar 2010, jimillar kudin kayayyakin da Sin ta shigo da su daga Afirka ya kai dala biliyan 1.35 karkashin wannan shirin ciki har da kayayyakin gona, duwatsu masu daraja, leda, tufafi da yaduna, kayayyakin gyaran injuna, karafa da kayayyakin da ke da nasaba da katako. Bugu da kari kasar Sin tana taimakawa kayayyakin Afirka su shigo kasuwannin Sin ta hanyar shirya kasuwannin baje kolin kayayyakin Afirka, bude cibiyoyin nune-nunen kayayyakin Afirka da ba su rufuna kyauta ko rage musu kudin hayar runfuna da dai sauran wasu garabasa.

Yanzu kasashen Sin da Afirka kasashe ne masu kokarin neman ci gaban masana'antu, don haka bukatarsu ta kasuwanni sanadiyar hadin gwiwar cinikayayya tsakaninsu tana da tasiri matuka. A bangaren Sin yadda Afirka ke fitar da danyen mai, ma'adinai, karafa, kayayyakin gona sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa ci gaban tattalin arzikin Sin da inganta rayuwar alummar Sinawa, kana a bangaren Afirka, kayayyaki da fasahohin sin sun taimaka wajen biyan bukatun ci gaban Afirka. Yayin da kayayyakin Afirka suka samu shiga kasuwar kasar Sin musamman ma lokacin da tattalin arzikinta ke ci gaba da bunkasa hakan ya samar da yanayin da ya dace ga albakartun da Afirka ke fitarwa zuwa kasuwa.

Bugu da kari kayayyakin Sin masu inganci da araha dake shiga Afirka sun taimaka wajen inganta rayuwar al'ummar Afirka kana sun taimakawa wasu kasashen Afirka magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China