in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

VII. Taka cikakkiyar rawa ta hanyar kiyaye tanade-tanaden FOCAC

A shekara ta 2000 ne Sin da kasashen Afirka suka kafa dandalin hadin gwiwa a tsakaninsu da ake kira (FOCAC) a takaice. Wanda ya tanadi tsare-tsaren tattaunawa da yin hadin gwiwa a matakai daban-daban, kamar tarukan ministoci, haduwar manyan jami'ai da tarukan 'yan kasuwa. Ya zuwa yanzu, a karkashin wannan tsarin an gudanar da tarukan ministoci da na bita guda. Sakamakon jajircewa a bangaren Sin da kasashen Afirka, FOCAC ya zamo wani muhimmin dandali na zaman haduwa da juna, kana wani tsarin samar da hadin gwiwa na zahiri a tsakanin Sin da Afirka. Ya haifar da yarda ta fannin siyasa, samar da hadin gwiwa, tare da daga matsayin dangantakarsu.

Tun taron FOCAC na ministoci da aka yi a shekara ta 2000, Sin ta lura da kalubaloli da yawan damar dake fuskantar ta da ma Afirka, gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakai na zurfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Afirka bisa yin hadin gwiwar dogon lokaci, tuntuba da girmama juna cikin daidaito. Wadannan matakai da suka dace da bukatun Afirka, suna nuni da irin kokarin gwamnatin kasar Sin ta fuskar kirkire-kirkire.

A taron ministoci na farko karkashin dandalin FOCAC, Sin ta sanar da cewar zata rage koma yafe bashinta dake kan kasashen Afirka, tare da karfafawa kamfunan kasar gwiwar zuba jari a Afirka tare da horas da kwararru na Afirkar. A taron ministocin dandalin FOCAC na biyu da aka yi a shekara ta 2003, Sin ta alkawarta kara taimakon da take baiwa Afirka, samar da hadin gwiwa ta fuskar bunkasa harkokin jama'a da kawar da dora haraji kan wasu kayayyakin da a kan fitar daga kasashen da suke koma baya a Afirka, masu alakar diflomasiyya da kasar Sin.

A taron da aka yi a Beijing, wanda ya kasance karo na uku na ministoci a dandalin FOCAC a shekara ta 2006, Sin ta sanar da wani shiri mai kunshe da matakai takwas dan karfafa hadin gwiwa ta zahiri tsakaninta da Afirka da ma yadda zata ba da goyon baya ga samun bunkasar Afirka, kamar a fannin kara ba da tallafi, samar da bashi, tallafawa kungiyar tarayyar Afirka (AU) wajen kafa wata tartibiyar cibiya, daga adadin kayayyakin da za a iya fitar da su zuwa Sin ba tare da biya musu haraji ba, kafa wani asusun bunkasa harkoki tsakanin Sin da Afirka, kafa shiyyoyin hadin gwiwa da cinikayyar ketare a kasashen Afirka, kafa cibiyoyin nune-nunen fasahohin ayyukan gona, sai kafa cibiyoyin kariya da shawo kan cutar zazzabin cizon sauro. A karshen shekara ta 2009 dukkanin wadannan matakai takwas da aka kudura an aiwatar da su bisa kokarin Sin da Afirka.

Cikin shekara ta 2009 Sin ta bayyana wani shirin mai matakai takwas a yayin taron ministoci na hudu a dandalin FOCAC, da suka shafi ayyukan gona, kariyar muhalli, kokarin jawo saka hannayen jari, rage bashi da ma yafe shi, ba da damar shiga kasuwanni, ilimi da kiwon lafiya. Wadannan matakai takwas da suka fi sa lura kan bunkasa matsayin zaman rayuwar al'umar Afirka, sanar da hadin kai ta fuskar ayyukan gona da bunkasa harkokin jama'a gami da daukaka matsayin Afirka na dogaro da kai, yana da burin taimakawa kasashen Afirka wajen shawo kan matsalolin dake gabansu, su kuma samu habaka mai dorewa tare da samun tabbacin ci gaban bunkasar tattalin arziki da walwala.

Tallafin na Sin ta hanyar dandalin F0CAC ya agazawa dukkan kasashen Afirka dake da huldar diflomasiyya da ita, tare da samar da alfanu a zahiri ga wadannan kasashe da ma al'ummunsu. A gaba, ta la'akari da samun moriyar juna da ci gaba,tattaunawar aminci, jajircewa da nuna hazaka. Gwamnatin kasar Sin tare da kasashen Afirka zasu ci gaba da karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu ta tsarin da dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka (FOCAC) ya tanada, tare da kokarin habaka wani muhimmin sabon kawance a tsakanin Sin da Afirka.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China