in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

IV. Hanyoyin gina jama'a

Ci gaba yana daya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar Afirka,amma rashin fasahohi da kwarewa sune muhimman abubuwan da ke kawo karan tsaye ga ci gabanta. Gwamnatin Sin ta dora muhimmanci ga bunkasa hanyoyin ci gaban Afirka,inda ta ke bunkasa jama'a da yin hadin gwiwa da Afirka,tura kwararru,matasa masu aikin jin kai zuwa Afirka don su taimakawa kasashen Afirka su inganta kokarinsu na zakulo kwararrun mutane.

Karfafa musaya ta fuskar ilimi da yin hadin gwiwa. Sin da Afirka sun yi musayar ilimi da yin hadin gwiwa damar data baiwa data taimaka wajen samun kwararrun mutane. Ya zuwa karshen shekarar 2009 Sin ta tallafa wajen gina makarantu 107 a Afirka,kana dalibai 29,465 daga Afirka sun samu guraben karo ilimi don yin karatu a Sin. A halin yanzu gwamnatin Sin ta yi tayin baiwa dalibai daga kasashen Afirka guraben karo ilimi 5000 kowa ce shekara. Har ila Sin ta kara karfafa hadin gwiwarta da kasashen Afirka a fannonin ilimi mai zurfi, ilimin sana'o'i, shirin karatu daga gida, gina dakunan binciken ilimin halittu na zamani, ilimin kwamfuta, ilimin Alkimiya, sarrafa da kuma adana abinci, aikin gona da gine-gine.

Sin ta taimakawa kasashen Afirka wajen samar musu da kwarewa kan harkokin gudanarwa ta hanyoyi dabam-dabam.A watan Yunin shekarar 2010, ta horas da sama da mutane dubu 30 daga kasahen Afirka a fannoni sama da 20 kamar tattalin arziki,tafiyar da harkokin mulkin gwamnati, aikin gona, kiwon dabbobi, masana'antar kifi, kiwon lafiya, kimiya da fasahar kyere-kyere da kiyaye muhalli. Baya ga wannan kuma,kamfanonin da ke Afirka sun horas da kwararrun ma'aikatan irin wadannan kasashe ta hanyar gina cibiyoyin horaswa da shirya kwasa-kwasan sanin makamar aiki da gayyato ma'aikatan Afirka su samu horo a Sin.

Shirya kwasa-kwasan horaswa: Sin ta shirya kwasa-kwasan horaswa da dama kan dashen itatuwa, kiwon dabbobi, kiwon kifaye, saka,zane da sarrafa leda. Alal misali ta shiryawa 'yan gudun hijira da daliban da aka kora daga makaranta saka da wasu kwasa-kwasai har ma da tallafawa marasa karfi a Libya wannan mataki ya bunkasa ci gaban iccen goro da saka kwando. Daga karshe wadanda suka samu horon suna samun kudin shigar da ya kai dala 150 a kowa ne wata kuma ya inganta rayuwarsu matuka.

Tura kwararru da matasa masu aikin jin kai zuwa Afirka: A karshen shekarar 2009, Sin ta tura manyan kwararru kan aikin gona zuwa kasashen Afirka 33 don taimaka musu tsara shirye-shiryen bunkasa aikin gona da basu jagoranci da kwasa-kwasan horaswa kan dabarun aikin gona.

Har ila Sin ta tura kwararru da zasu sa-ido kan yadda ake tafiyar da ayyukan da Sin ta tallafa aka samar, horas da kananan ma'aikatan da ke tafiyar da harkokin gudanarwa, da taimakawa kasashen Afirka kan yadda za su kula da ayyukansu da kansu. Bugu da kari, Sin ta hada kai da shirin samar da abinci na MDD, sanya hannu kan yarjejeniyar dangantakar abokantaka da kasashen Murutania, Ghana, Habasha, Gabon, Saliyo, Mali da Najeriya. Sannan ta tura kwararru sama da 600 kan aikin gona zuwa wadannan kasashe. A karshen shekarar 2009 Sin ta tura matasa masu aikin sa-kai zuwa Afirka inda suke koyar da harshen Sinanci kyauta, samar da ilimin jinya da lafiyar jama'a, koyar da ilimin motsa jiki, da ilimin kwanfuta da aikin ceto na kasa da kasa.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China