in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
RAHOTON HADIN GWIWAR TATTALIN ARZIKI DA CINIKAYYA TSAKANIN KASASHEN SIN DA AFIRKA
2010-12-31 14:19:26 cri

VI. Fadada bigiren hadin gwiwar Sin da Afirka.

A shekarun baya-bayan nan, wasu sabbin sassan yin hadin gwiwa tsakani Sin da Afirka, musamman harkar da ta shafi aikin banki, yawon bude ido, sifirin jiragen sama da batun kare muhalli, sun nuna kyakkyawar alamar bunkasuwa. Bugu da kari, a cikin tsarin sada zumunci a mabambantan fannoni, Sin da kasashen Afirka sun karfafa hadin gwiwa da tallafawa juna a sassa da dama da ake nuna damuwa a duniya, ciki har da ayyukan shawo kan dumamar yanayi.

Hadin gwiwa a fannin aikin banki. Gwamnatin kasar Sin ta goyawa kokarin cibiyoyin kudin Sin da na Afirka baya domin su tabbatar da ayyukansu na hadin gwiwa da musaya, tare da samar da nagartattun ayyukan da suka shafi kudi dan amfanin kamfunan sassan biyu. Bankunan China Development Bank, Export-Import Bank of China, Industrial and Commercial Bank of China, Bank of China da China Construction Bank duk suna gudanar da harkokinsu yau a nahiyar Afirka, wadanda suka hada da samar da zarafin kasa da kasa, cinikayya da samar da kudi, da ma musamman yin hada-hadar kudi a sassan harhada kayayyaki, makamashi, sadarwa, wutar lantarki, samar da ruwa, sifiri, ayyukan gona da tsare-tsare. Cibiyoyin kudi na kasar Sin sun kafa rassa ko kuma ofisoshinsu na wakilci a kasashen Zambia, Afirka ta kudu da Masar. Sin ta hada karfi da bankin ADB na raya kasashen Afirka da WADB, na raya yammacin Afirka wajen goyon bayan yunkurin rage radadin fatara tare da samun bunkasar Afirka ta hanyar taimakawa da kudi, kawar da bashi da kafa asusun tabbatar da ayyukan hadin gwiwa a fagen fasaha. A halin yanzu, cibiyoyin kudin kasashen Afirka su ma sun fadada kasuwancinsu zuwa kasar Sin. Ya zuwa karshen shekara ta 2009, bankuna shida na wasu kasashen Afirka biyar ciki da Masar, Morocco, Kamaru, Afirka ta kudu da Najeriya, sun kafa rassa ko ofisoshin wakilci a Sin.

Hadin gwiwa a fannin yawon bude ido. Harkar yawon ido na daya daga cikin masana'antu mafiya muhimmanci masu tasowa a kasashen Afirka, kana wata sabuwar hanyar bunkasa cinikayya tsakanin Sin da Afirka. A aikace gwamnatin kasar Sin ta sauke nauyin dake kanta game da hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin yawon bude ido.Tun bayan da Masar ta zamo kasa ta farko da ta samu matsayin shedar wajen da aka amincewa zuwa yawon bude ido (ADS) daga babban yankin kasar Sin a shekara ta 2002, baki daya, ya zuwa karshen shekara ta 2009, kasashen Afirka da yankuna da suka samu irin wannan matsayi sun kai 28. A shekara ta 2009, wasu Sinawa daga babban yankin kasar su dubu 381 ne suka ziyarci Afirka, a matsayin zangon farko na bulaguronsu, adadin da ya yi sama da kashi 18.5, kan makamancin lokaci na shekarun baya. Yayin da adadin 'yan Afirka da suka yi bulaguro zuwa Sin a shekara ta 2009 ya karu da kashi 6 kan na shekara ta 2008, wanda ya kai mutane dubu 401. Haka ma, kamfunan Sin sun kakkafa cibiyoyin bulaguro da dakunan cin abinci, tare da sa hannu wajen gina otal-otal da kulawa da su a Afirka.

Hadin gwiwa a fannin sufirin jaragen sama. Gwamnatin Sin ta baiwa kamfunan zirga-zirgar jiragen sama na sassan biyu kwarin gwiwar kafawa da inganta dangantakarsu ta hadin gwiwa, tare da samar da zirga-zirga ta kai tsaye a tsakanin Sin da Afirka, dan daukar fasinjoji da kayayyaki. Ya zuwa karshen shekara ta 2009, Sin ta sanya hannu da wasu kasashen Afirka 15, kan yarjejeniyar sifirin fasinjoji ta jiragen sama. Cikin wadannan kasashe har da Habasha(Ethiopia), Angola, Zambia da Afirka ta kudu, tare da tuntubar wasu kasashen 6, kamar Seychelles, Libya da Uganda kan irin wannan yarjejeniya. Kamfunan jiragen sama na Masar, Habasha,Zimbabwe, Kenya da Aljeriya sun bubbude tsarin sifirinsu zuwa biranen Beijing da Guangzhou, yayin da kamfunan jiragen sama na Sin suke da tsarin sifirin kai tsaye tsakanin Beijing da biranen Legas na Najeriya, Luanda na Angola da Khartoum na Sudan. Bugu da kari, sashin kula harkokin sifirin jiragen sama na kasar Sin ya samar da tallafi ga Afirka ta hanyoyi da yawa, wadanda suka hada da kungiyar kula da sifirin jiragen sama ta kasa da kasa (ICAO). Sin ta alkawarta ba da dalar Amurka dubu 100 ga kungiyar ta ICAO daga shekara ta 2008 zuwa ta 2011, dan aiwatar da cikakken shirin da ya shafi yanki dan tabbatar da kariya ga harkar sifirin jiragen sama a Afirka.

Hadin gwiwa kan kare muhalli. Batutuwan samar da kariya ga muhalli gami da hanyar shawo kan sauyin yanayi,su ne suka tsayawa duniya a wuya. A karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, sassan biyu sun gudanar da taron hadin gwiwar samar da kariya ga muhalli tsakanin Sin da Afirka, tare da aiwatar da shirin ba da horo ga jama'a dan ba da kariya ga muhalli, da kafa cibiyar kula da muhalli ta Sin da Afirka ta UNEP. Gwamnatin kasar Sin ta tsara shirin kulla kawance tsakani Sin da Afirka wajen magance sauyin yanayi, da karfafa hadin gwiwa a bigirorin kula da yanayi ta tauraron dan Adam, bunkasawa da kuma yin amfani da sabbin hanyoyin samun makamashi, karewa da kuma shawo kan kwararowar Hamada da kare muhallin birane. Sin da Afirka sun yi wata gagarumar musayar ra'ayoyi kan batutuwan da suka shafi muhalli kamar tattaunawar kasa da kasa kan sauyin yanayi, dan kare muradun kasashe masu tasowa. Sin ta goyi bayan korafe-korafen da suka dace na kasashen Afirka game da shawo kan sauyin yanayi, tare da kula da damuwar kasashen Afirka kan burin rage ayyukan da kan gurbata iska na tsawon lokaci. Haka kuma gwamnatin kasar Sin tayi alkawari ba zata yi gogayya da kasashen Afirka ba wajen neman taimakon kudi, maimakon hakan sai ma ta basu, daidai gwargwadon bukatunsu, samar da taimakon kudi, fasaha da horas da ma'aikata. A halin yanzu, Sin ta hada shirye-shiryen hadin gwiwa da wasu kasashen Afirka a sassan fasahar samar da gas ta hanyar amfani da takin gargajiya, samar da lantarki ta amfani da ruwa, hasken rana da iska.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China