An kira cikakken zaman taron wakilan jam'iyyar SWAPO karo na shida a birnin Windheok, a tsakanin ranar 23 zuwa ranar 26 ga watan nan da muke ciki, inda aka zabi sabon shugaban jam'iyyar, da kuma mataimakinsa da dai sauran jami'an jam'iyyar.
Kaza lika mataimakin firaministan kasar na yanzu, kana ministan dake kula da harkokin dangantakar diflomasiyya da hadin gwiwar kasa da kasa Netumbo Nandi Ndaitwah, shi ne ya lashe zaben mataimakin shugaban jam'iyyar ta SWAPO mai mulkin kasar ta Namibia. (Maryam)