Sakataren jam'iyyar na kasa Nangolo Mbumba ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi, yana mai cewa daukar wannan mataki zai baiwa matasa damar zama masu kyawawan halaye. kazalika makarantar za ta rika koyar da darussan tarihin kasar, da fayyace manufofin jam'iyyar ta Swapo, ta yadda hakan zai bada damar samun magada a jam'iyyar bayan shudewar wadanda ke rike da ita a yanzu.
A bara mai dai jami'in jam'iyyar mai kula da harkokin yada bayanai Helmut Angula, ya bayyana burin da Swapon ke da shi, na samar da jagorori da za su iya wakiltar jam'iyyar bisa kwarewa, tare da nuna kyakkyawan misali.
Jam'iyyar Swapo ce dai ke mulkin Namibia, tun bayan samun 'yancin kan kasar a shekara ta 1990. (Saminu Hassan)