in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Sin ya gana da mataimakiyar firaministan kasar Namibia
2017-04-11 20:10:48 cri
A yau Talata ne a nan birnin Beijing, mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao, ya gana da mataimakiyar firaministan kasar Namibia, kuma ministar harkokin wajen kasar Netumbo Nandi-Ndaitwah.

A yayin ganawar, Li Yuanchao ya bayyana cewa, kasar Sin da Namibia suna sada zumunta da juna, kuma a shekarun nan bangarorin biyu sun yi mu'amala da hadin gwiwa, tare da samun nasarori a fannoni daban daban, kana sun fahimci juna, da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu.

Kaza lika kuma ya yi fatan bangarorin biyu za su kara imani da juna a fannin siyasa, da yin mu'amala da juna kan fasahohin gudanar da harkokin kasa, da amfani da fifikon su na zurfafa hadin gwiwa, da yin mu'amalar al'adu, don sa kaimi ga bunkasa dangantakar hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin Sin da Namibia.

A nata bangare, Madam Ndaitwah ta bayyana cewa, yayin da ake ci gaba da sada zumunta a tsakanin kasashen biyu cikin tsawon lokaci, tana fatan bangarorin biyu za su kara mu'amala da hadin gwiwa a fannonin samar da kayayyaki, da inganta aikin gona, da horar da kwararru, da harkokin kasa da kasa da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China