in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Namibia ya yi gargadi game da rashin aikin yi a tsakanin matasa
2017-04-13 09:25:11 cri
Shugaban kasar Namibia Hage Geingob, ya ce yawaitar rashin aikin yi a tsakanin matasa ka iya yi wa zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar tarnaki.

Da yake jawabi game da halin da kasar ke ciki a gaban majalisar dokokin kasar, Hage Geingob, ya alakanta rashin ayyukan yi da yadda aka fi zuba jari a bangarorin hakar ma'adainai da manyan kamfanoni da suka fi amfani da injuna.

Ya ce a yanzu adadin rashin aikin yi a kasar ya kai kashi 39.2 cikin dari.

Shugaban kasar ya ce wani muhimmin matakin da gwamnati ta dauka na magance rashin aikin yi a tsakanin matasa shi ne, inganta ba da horo kan sana'o'in hannu da fasahohi.

Ya ce a bara, sama da dalibai 24,000 ne aka dauka a cibiyoyin koyar da sana'o'i, adadin da ya zarce 16,000 da aka yi niyyar dauka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China