Zhang Gaoli ya bayyana cewa, Sin za ta karfafawa kamfanonin kasarta gwiwar da su zo su zuba jari a kasar Namibia, kana su hada kai da Namibia a fannonin bullo da tsare-tsare, da harkokin kudi, da dokoki da sauransu don samar da kyakkyawan yanayin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Muhimmin aikin inganta hadin gwiwar kasashen biyu a yanzu shi ne aiwatar da ayyukan da aka tsara a gun taron koli na dandanlin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka na birnin Johannesburg. Ya ce Sin ta dora muhimmanci sosai kan jerin matakan da kasar Namibia ta gabatar, wadanda take son gudanarwa da farko. Kana Sin tana fatan hukumomin kasashen biyu da abin ya shafa za su kara hada kai, tare da gudanar da ayyukan dake shafar tattalin arziki da zamantakewar al'umma yadda ya kamata.
A nasa bangare, shugaba Geingob na Namibia ya ce, yana fatan kasar Sin za ta taimakawa kasarsa a fannonin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa, aikin gona, kiwon lafiya, ba da ilmi, makamashi da sauransu, don taimakawa kasar Namibia samun bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma. (Zainab Zhang)