in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da takwararsa ta kasar Namibia
2017-09-20 14:04:57 cri

Jiya Talata ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwararsa ta Namibia kana mataimakiyar firaministar kasar Netumbo Nandi-Ndaitwah, yayin da yake halartar babban taron MDD a birnin New York na kasar Amurka.

A yayin ganawar, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin na da aniyar inganta cudanya tsakanin manyan kososhin kasashen biyu, da kyautata hadin gwiwa tsakaninsu daga dukkan fannoni, da kuma aiwatar da shirye-shiryen da aka tsara yayin taron dandantalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afirka na FOCAC yadda ya kamata, a kokarin samar da goyon baya da tallafi ga Namibia, ta yadda za ta iya raya ayyukan gona na zamani da masana'antunta.

A nata bangaren, Madam Ndaitwah ta furta cewa, kasar Namibia na son ci gaba da sa hannu cikin ayyukan hadin gwiwa a karkashin inuwar tsarin FOCAC, domin ciyar da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa gaba, da kuma amfana wa jama'arsu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China