in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibia za ta kafa rundunar sojan sama ta yaki da farauta ba bisa ka'ida ba
2017-08-10 10:17:34 cri
A jiya Laraba ne ministan muhalli da yawon shakatawa na kasar Namibia Pohamba Shifeta, ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka yi a birnin Windhoek fadar mulkin kasar cewa, kasarsa za ta kafa wata rundunar sojan sama ta yaki da masu farautar dabbobin daji ba bisa ka'ida ba, domin karfafa hadin gwiwar dake tsakanin sojojin kasa da na sama, a yayin da suke gudanar da ayyukan sintiri, ta yadda za a warware matsalar masu haramtacciyar sana'ar nan ta farauta ba bisa ka'ida ba.

Mr. Shifeta ya ce, tuni ma'aikatar harkokin kare muhalli da yawon shakatawa ta nemi wasu matukan jirgin sama, wadanda za su fara ayyukan sintiri a lambun shan iska na kasar dake Etosha, da kuma lambun shan iska na kasar dake Babatwa.

Bisa kididdigar da ma'aikatar muhalli da yawon shakatawa ta yi, an ce a shekarar 2014 kadai, an sace karkanda guda 61, da wasu guda 91 a shekarar 2015, kana da karin wasu 63 a shekarar 2016.

A sa'i daya kuma, an sace giwaye guda 78 a shekarar 2014, da wasu 49 a 2015, tare da karin wasu 101 a shekarar 2016. Kuma an sace galibinsu ne daga lambunan shan iska na Etosha da na Babatwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China