in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta hada kai da Namibia wajen yaki da farautar namun daji
2017-03-03 19:58:44 cri

Jami'in jakadancin kasar Sin dake Namibia Li Nan, ya ce kasar Sin za ta yi hadin gwiwa da Namibia, wajen yaki da farautar namun daji ba bisa ka'ida ba, da bada kariya ta musamman ga albarkatun daji.

Kalaman na Mr. Li dai na zuwa ne a ranar kasa da kasa ta kare albarkatun daji wadda ake gudanarwa ko wace shekara, a ranar 3 ga watan nan na Maris.

Mr. Li ya ce Sin za ta goyi bayan Namibia wajen sauya fasalin dokokin kasar na kare muhalli, kuma ba za ta bada ko wace irin kariya, ga masu karya dokokin farautar dabbobin daji ba.

A nasa tsokaci game da wannan batu, ministan ma'aikatar muhalli da yawon shakatawa a Namibia Tommy Nambahu, cewa ya yi ya zama wajibi hukumomin dake aiwatar da dokoki, su kara zage damtse wajen hukunta masu karya dokar farautar dabbobi, musamman giwaye da bauna.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China