Wata sanarwa da asusun ya fitar ta ce, mutane dari takwas da casa'in da hudu ne suka jikkata sanadiyyar haddura dari hudu da tamanin da suka auku a kan titunan fadin kasar. Adadin ya ragu idan aka kwatanta da na bara da mutane dubu daya da sittin da biyu suka jikkata sanadiyyar haddura dari biyar da talatin.
Adadin wadanda suka rasa rayukansu kuwa ya ragu ne da guda daya, inda a bara aka samu mutuwar mutane casa'in da hudu.
A kokorin sake rage aukuwar haddura a bana yayin da ake kokarin komawa makaranta da kuma aiki a kasar, asusun ya sanar da cewa zai fara aiki a wasu titunan kasar domin tabbatar da matafiya sun isa inda suke son zuwa lami lafiya. (Fa''iza Mustapha)