in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen Zimbabwe da sojojin tsaron kasa sun musanta yin juyin mulki a kasar
2017-11-17 15:08:55 cri
A ranar 16 ga wata da yamma, ma'aikatar harkokin wajen kasar Zimbabwe, da rundunar sojojin tsaron kasar, sun kira taron manema labarai, inda suka musanta aukuwar juyin mulki a kasar, suna masu cewa, sojojin kasar suna bauta wa shugaba Mugabe, babu bukatar al'ummomin kasar su damu game da tsaron shugaban kasar.

Jakadun kasashe da dama dake kasar Zimbabwe sun halarci wannan taro.

Sakataren gudanarwa na ma'aikatar harkokin wajen kasar Joey Bimha ya bayyana cewa, a safiyar ranar 15, sojojin kasar sun dauki matakan soja, domin karbe ikon muhimman hukumomin gwamnatin kasar, da kuma kama wadanda suke haifar da illa ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'ummar kasar. An kuma ba da umurni cewa, kada a dauki matakai da za su haifar da zubar da jini, don haka ya zuwa yanzu, babu wanda ya ji rauni ko rasa rai.

Mr. Bimha ya kuma musanta labarin cewar, juyin mulki ne aka yi a kasar, ya kuma jaddada cewa, matakan da sojojin kasar suka dauka na da nufin gyara kuskuren da jam'iyya mai mulki da gwamnatin kasar suka aikata ne, kuma za su ci gaba da martaba shugaba Mugabe, kuma shi da dukkan iyalansa suna cikin koshin lafiya.

A halin yanzu kuma, ana gudanar da ayyukan gwamnatin kasar yadda ya kamata, yayin da al'ummomin kasar ke cikin kwanciyar hankali.

Kungiyar raya kudancin kasashen Afirka ta SADC ta kira taron tattaunawa, game da yanayin siyasar kasar ta Zimbabwe da yammacin ranar 16 ga wata a birnin Gaborone na kasar Botswana, inda wakilan taron suka yi kira ga kungiyar da ta gaggauta shirya wani taron kolin musamman, tare da bukatar bangarorin da sabanin kasar Zimbabwe ya shafa, da su warware matsalar ta hanyar lumana. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China