in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ji karar ababan fashewa a Zimbabwe, sai dai an musanta yunkurin juyin mulki
2017-11-15 13:50:17 cri
Da sanyin safiyar yau Laraba an ji karar ababan fashewa a tsakiyar birnin Harare, kwanaki biyu bayan da sojojin kasar suka yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar da nufin kawo karshen takaddamar siyasar kasar, sai dai manyan dakarun sojin kasar Zimbabwen sun musanta yunkurin juyin mulki a kasar.

A safiyar Larabar hafsoshin sojin kasar Zimbabwe sun bada sanarwa ta gidan talabijin din kasar cewa, ba su kwace ikon gwamnatin kasar ba, amma suna yunkurin zakulo wasu masu laifi ne dake kewaye da gwamnatin shugaba Robert Mugabe na kasar.

A jawabin da manyan jami'an sojin kasar suka watsa kai tsaye ta gidan talabijin na kasar sun ayyana cewa, shugaba Mugabe da iyalansa suna cikin tsaro da kwanciyar hankali, kuma dakarun sojin suna ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China