Ministan yada labaran kasar Simon Khaya Moyo, ya shedawa taron manema labarai a babban birnin kasar cewa, korar ta mista Emmerson ta fara aiki ne nan take.
Moyo ya ce, bisa dokar kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwe, shugaba Robert Mugabe ya tube mataimakinsa Emmerson Mnangagwa daga kan mukaminsa na mataimakin shugaban kasar nan take.
Ya ce ta bayyana karara cewa mataimakin shugaban kasar ba ya gudanar da ayyukan dake wuyansa yadda ya kamata. Kana a koda yaushe yana nuna halin rashin da'a, da rashin girmamawa, da yaudara, da kuma rashin tabbas. Sannan yana nuna rashin gashiya wajen tafiyar da ayyukansa.
Mugabe ya nada Mnangagwa a matsayin mataimakinsa ne a shekarar 2014, bayan da ya sallami tsahon mataimakinsa Joice Mujuru bisa zarginsa da yunkurin haifar da baraka da kuma kokarin yi masa juyin mulki. (Ahmad Fagam)