in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji a Zimbabwe sun yiwa fadar shugaban kasar kawanya
2017-11-15 19:09:37 cri
Rahotanni daga Zimbabwe na cewa, da sanyin safiyar yau ne sojoji suka yiwa fadar shugaban kasa da ginin majalisar dokokin kasar dake Harare,babban birnin kasar kawanya da motoci masu sulke, yayin da jirage masu saukar ungulu kuma ke ta yin shawagi a tsakiyar birnin, bayan da sojoji suka sanar da kwace ikon dukkan hukumomin gwamnati.

Yanzu haka dai, babu ko da 'yan sanda a kan tituna,idan ban da sojoji da ke kula da zirga-zirgar ababan hawa, wasu rahotanni da ba a tabbatar ba na cewa, ana tsare da wasu ministoci da manyan jami'an jam'iyyar Zanu-PF mai mulkin kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China