Shugaba Zuma ya ce akwai bukatar rundunar sojojin Zimbabwe ta dauki matakai na lumana, wajen warware takaddamar siyasa da ta dabaibaye kasar, sai dai a cewarsa ya dace dukkanin matakan da za a dauka su kasance na lumana, ba kuma wadanda za su haifar da illa ga harkokin tsaron kasar ba.
Ya ce kungiyar bunkasa yankin kudancin Afirka ta SADC, za ta ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki a Zimbabwe, za kuma ta bada taimako a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, kamar yadda hakan ke cikin kudurorin kafa ta.
Yanzu haka dai Afirka ta kudun ce ke jagorancin kungiyar ta SADC. (Saminu Hassan)