in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya bukaci a martaba kundin tsarin mulkin Zimbabwe
2017-11-16 10:24:38 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci a kai zuciya nesa, a kuma martaba kundin tsarin mulkin Zimbabwe, a gabar da kasar ke fuskantar danbarwar siyasa.

Shugaba Buhari ya yi wannan kira ne a jiya Laraba cikin wata sanarwa da fadar gwamnatinsa ta fitar, yana mai jan hankalin shugabannin siyasa da tsagin rundunar sojin Zimbabwe, da su kaucewa daukar matakai da ka iya jefa kasar cikin mummunan yanayi maras dalili.

Ya ce kamata ya yi a dauki dukkanin matakai na warware takaddamar da sassan kasar ke fuskanta ta hanyar martaba kundin tsarin mulkin kasar, domin ta haka ne kawai za a kaucewa jefa kasar cikin halin ha'ula'i, wanda kuma ka iya shafar sauran kasashe dake yankin. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China