Shugaban hukumar zartaswar kungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat, shi ne ya yi wannan kira a jiya Laraba, yana mai cewa kungiyar na bibiyar halin da ake ciki a Zimbabwe, bayan da sojoji suka amshe iko a jiya.
Mr. Mahamat ya ce "Ina kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki, da su dauki matakan warware sabani ta hanyar martaba dokokin kundin tsarin mulkin kasar, da ma sauran tanaje tanaje na kungiyar ta AU, ciki hadda sashen da ya ayyana bukatar martaba mulkin dimokaradiyya na nahiyar Afirka, da harkar zabe, tare da gudanar da sahihiyar gwamnati. (Saminu Hassan)