in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Robert Mugabe ya bayyana a karon farko tun bayan amshe madafun iko
2017-11-17 10:41:39 cri
Shugaban kasar Zimbabwe da a yanzu haka sojojin kasar sa ke yiwa daurin talala, ya bayyana ta wasu kafofin watsa labarai a karon farko, tun bayan da aka amshe iko daga hannunsa.

Jaridar Herald ta kasar Zimbabwe, ta wallafa hoton shugaban na ganawa da jagoran rundunar tsaron kasar Constantino Chiwenga, da kuma wasu jakadun yankin kudancin Afirka a fadar gwamnatin kasar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, ministan tsaron kasar Sydney Sekeramayi, da karamin ministan tsaron cikin gidan kasar Kembo Mohadi, na cikin wadanda suka halarci taron na jiya Alhamis. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China