in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron kasar Sin ya gana da kwamandan sojojin kasar Zimbabwe
2017-11-10 21:33:17 cri
A yau Juma'a ne wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan tsaron kasar Chang Wanquan, ya gana da kwamandan rundunar sojojin kasar Zimbabwe Constantine Guveya Chiwenga a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar tasu, Mr. Chang ya ce, kasarsa na fatan kokari tare da bangaren Zimbabwe, don tabbatar da ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a dukkan fannoni, tare kuma da karfafa matsayin hadin kai a fannin aikin soja.

A nasa bangaren Chiwenga ya bayyana cewa, kasar Zimbabwe na mai da hankali kan zumuncin dake tsakanin kasashen biyu da ma rundunonin sojansu, tana kuma fatan ci gaba da kokari tare da Sin, don ciyar da dangantakar dake tsakaninsu gaba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China