in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren Janar na MDD ya yi kira da a kwantar da hankali a Zimbabwe
2017-11-17 10:47:02 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kwantar da hankali a Zimbabwe, bayan sojoji sun yi wa shugaban kasar Robert Mugabe mai shekaru 93 daurin talala.

Kakakin Sakatare Janar din Stephane Dujarric, ya ce Antonio Guterres na bibiyar yadda al'amura ke tafiya a Zimbabwe, inda ya yi kira da a ci gaba da zaman lafiya a kasar.

Ya jadadda muhimmancin warware takaddamar siyasar cikin ruwan sanyi, ta hanyoyin da suka hada da hawan teburin sulhu bisa biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar.

Sakatare Janar din ya kuma yi maraba da yunkurin Kungiyar raya kasashen kudancin Afrika, na shiga tsakani wajen samar da masalaha cikin ruwan sanyi. Inda ya ce zai ci gaba da tuntubar shugaban hukumar Tarayyar Afrika AU da shugabannin yankuna domin mara baya ga irin wannan yunkuri.

Sanarwar da kakakin nasa ya fitar ta kuma ruwaito Antonio Guterres na jadadda kudurin MDD na ci gaba da mara baya ga kokarin kasar Zimbabwe na karfafa tsarin demokradiyya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China