in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FAO ta jaddada muhimmancin fuskantar sauyin yanayi domin raya ayyukan gona
2017-11-16 10:54:52 cri
Kwanan baya, hukumar abinci da ayyukan gona ta MDD wato FAO ta fidda wani rahoto dake nuna cewa, adadin iska da abubuwa masu gurbata muhalli, wanda hukumomin ayyukan gona za su fidda zai karu a nan gaba, lamarin da zai kara sauya yanayi a duniya, muddin dai a yi amfani da fasahohin zamani na kare muhalli, wajen gudanar da ayyukan gona a kasashen duniya.

Haka zalika, an ruwaito jawabin babban sakataren hukumar FAO Jose Graziano da Silva, wanda ya ce sauyin yanayi ya haddasa matsalolin karancin abinci, da talauci ga dimbin mutane, don haka ya kamata a fuskanci wannan matsala yadda ya kamata, yayin da ake daukar karin matakai wajen warware matsalar.

Hukumar FAO ta sanar da cewa, adadin masu fama da karancin abinci ya karu karo na farko cikin shekaru 10 da suka gabata, kuma a ko wace rana, akwai mutane kimanin miliyan 815 da ba sa iya samun isasshen abinci a duniya.

Babban dalilan da suka haddasa matsalar su ne rikice-rikice, da raguwar tattalin arziki da kuma sauyin yanayi da dai sauransu, musamman ma matsalar fari da mutanen Afirka suke fama da ita. Bisa hasashen da kwamitin musamman dake kula da sauyin yanayi tsakanin gwamnatocin kasa da kasa ta yi, an ce, ya zuwa shekarar 2050, mai yiwuwa ne, adadin masu fama da karancin abinci zai karu da kashi 20 bisa dari, sakamakon sauyin yanayi a duniya.(Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China