in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO: Yankunan karkara su ne jigon ci gaban tattalin arzikin kasashe masu tasowa
2017-10-10 10:53:36 cri
Wani sabon rahoton da hukumar samar da abinci ta duniya ta fitar ya nuna cewa, idan aka yi kyakkyawan amfani da miliyoyin matasa dake kasashe masu tasowa wajen shigar da su ayyukan dogaro da kai, nan da wasu gwamman shekaru masu zuwa, babu bukatar a samu kwararar jama'a daga yankunan karkara zuwa birane saboda talauci.

Rahoton ya kara da cewa, yankunan karkara suna da damammaki masu yawa na yiwuwar samun bunkasuwar tattalin arziki wanda yake da nasaba da ayyukan samar da abinci, kamar yadda shirin samar da abinci da ayyukan gona na 2017 ya bayyana. Shirin ya ce kasancewar mafi yawan al'ummar duniya dake fama da kangin talauci da yunwa su ne mutanen dake zaune a yankunan karkara, cimma nasarar ajandar samar da ci gaba nan da shekarar 2030 ya dogara ne kan sake komawa wadannan yankuna da aka yi watsi da su.

Idan ana son cimma wannan buri, dole ne sai an kawo karshen daina amfani da kayayyakin aikin gona marasa inganci, da cika gibin karancin masana'antu a mafi yawan wuraren, da batun tsara yawan al'umma, da mayar da kauyuka zuwa birane, dukkan wadannan sun kasance manyan kalubaloli ga kasashe masu tasowa wajen gaza samar da isasshen abinci ga 'yan kasa da kuma samar musu ayyukan dogaro da kai.

Rahoton ya lura cewa, farfado da tattalin arzikin yankunan karkara ya ta'allaka ne ga taimakawa miliyoyin jama'a mazauna yankunan karkara domin su samu damar fita daga kangin talauci tun daga shekarar 1990. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China