in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FAO ta yi kira da a kara zage damtse wajen magance matsalar fari da ta shafi wasu kasashen Afrika
2017-04-29 12:38:44 cri
Hukumar FAO mai kula da harkokin abinci da aikin gona a duniya, ta yi kira da a kara zage damtse, wajen kai dauki ga matsalar fari da ake fuskanta a kasasehen Afrika da suka hada da Nijeriya da Somaliya da Sudan ta Kudu da kuma Yemen.

Hukumar ta yi gargadi a rahotonta na baya-bayan nan na cikin watan Afrilu cewa, idan ba a dauki mataki ba, miliyoyin mutane ne za su iya mutuwa a kasashen hudu, inda mutane kimanin miliyan 30 ke cikin matsananciyar yunwa.

Tuni aka ayyana fari a hukumance, a wasu sassa na kasar Sudan ta Kudu, inda matsalar ta shafi mutane 100,000, kuma sama da mutane miliyan 5.5 ne za su yi fama da rashin abinci zuwa watan Yuli mai zuwa.

Matakin karancin abinci da ake fuskanta a kasashen hudu, alamu ne dake nuna karancin zuba jari a fannin harkokin noma da na inganta walwar jama'a.

Baya ga haka, rikice-rikice da farin na tilastawa mutane tserewa matsugunansu .

A yankin arewa maso gabashin Nijeriya kuwa, hukumomin na hada hannu wajen tabbatar da mutane da ke cikin halin yunwa, sun samu taimakon abinci da suke bukata da kuma na yadda za su samar da abincin da kansu.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China