Daraktan FAO ya ce, shirin na hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa ya kasance a matsayin wata hanyar samar da cigaba wadda ta sha banban da tsarin gargajiya da abokan hulda ke amfani da su. Wannan shirin ya kasance a matsayin wata mikakkiyar hanyar hadin gwiwa da tabbatar da hadin kai tsakanin bangarorin da abin ya shafa.
Jose ya yi wannan tsokaci ne a lokacin taron FAO wanda aka gudanar domin nazartar irin nasarorin da aka cimma karkashin shirin FAO da hadin gwiwar kasar Sin da kasashe masu tasowa, da kuma duba hanyoyin da za'a kara shigar da wasu karin kasashen duniya da ma kungiyoyin kasa da kasa cikin wannan shiri na hadin gwiwa.
A cewar FAO, Sin ita ce kasa ta farko da ta shiga shirin hadin gwiwar FAO da na kasashe masu tasowa tun lokacin da aka kafa shirin shekaru sama da 20 da suka gabata, kuma kasar Sin ta tura kwararru sama da 1,000 da wasu likitoci zuwa kasashen Afrika 26, da nahiyar Asiya da kudancin Pacific, da Latin America da Caribbean, karkashin shirin hadin gwiwa FAO da kasar Sin da kasashe masu tasowa.(Ahmad)