in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi kira da a kara daukar matakai na tinkarar sauyin yanayi
2017-11-11 15:00:53 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana fatansa na ganin gamayyar kasa da kasa sun kara daukar kwararan matakan tunkarar sauyin yanayi.

Mr. Guterres ya yi wannan kira ne a jiya, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai kafin ya tashi zuwa birnin Bonn na kasar Jamus domin halartar taron MDD da za a yi dangane da sauyin yanayi.

Babban sakataren ya kara da cewa, alkaluman da aka samar da dumi-duminsu sun gargadi kasashen duniya game da matsalar sauyin yanayi, don haka, ya zama dole su gaggauta daukar matakai tare da samun karin kwarin gwiwa.

Har ila yau, ya yi kira da a rage yawan hayakin dumama yanayi da ake fitarwa da kaso 25% kafin shekarar 2020. Baya ga haka, ya kuma yi kira da a cika alkawarin da aka dauka na samar da dala biliyan 100 ga kasashe masu tasowa a kowace shekara, tare kuma da taimakawa kasashen da matsalar sauyin yanayi ta fi addaba, inganta kwarewarsu kan tunkarar matsalar.

A ranar 30 ga watan Oktoba ne, hukumar kula da yanayin duniya ta fitar da rahoton cewa, a shekarar 2016, yawan hayakin Carbon Dioxide da ke cikin iska ya karu, har ma ya kai matsayin koli a cikin shekaru dubu 800 da suka wuce.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China